Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Mai shekara 90 ta yi shirin zabe a Gayam

    Gado mai shekara 90 na shirin yin zabe a Gayam Lafiya, Nasarawa

  2. Wasu na jiran kada kuri'a a Nasarawa

    Wasu na jiran kada kuri'a a mazabar Gayam da ke birnin Lafiya na jihar Nasarawa.

  3. Labarai da dumi-dumi, Shin Buhari ya karya dokar zabe?

    Hotuna sun nuna yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya kada kuri'a inda ya zabi kansa.

    Mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya dauki hotunan takardun kada kuri'ar Buhari, wadanda suka nuna cewa ya zabi kansa.

    Hukumar zaben Najeriya dai tana ba da shawara kada masu kada kuri'a su bayyana wanda suka zaba, saboda hakan ya saba tsarin tarbiyyar dimokradiyya.

  4. Masu zabe a Abuja

    Masu zabe sun yi layi a mazabar makarantar firamare da ke Utako a Abuja, babban birnin Najeriya.

  5. Ana kada kuri'a a mazabar Atiku

    Wani dattijo da aka bai wa wajen zama domin kada kuri'a a mazabar dan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da ke Yola, Adamawa.

  6. Ni zan lashe zaben Najeriya - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shi ne zai lashe zaben Najeriya.

    Da yake amsa tambayar da wakilin BBC ya yi masa kan ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "Zan taya kaina murna" saboda ni zan ci zabe.

  7. Kan tituna a Makurdi babu mutane

    Mutane sun kaurace wa titunan Makurdi, babban birnin jihar Benue sakamakon zabukan da ake gudanarwa a duk fadin Najeriya.

  8. Yadda muke gabatar da shirye-shirye kai tsaye a radiyo

  9. Katunan zaben da suka lalace

    Wannan hoton wani akwatin da ke dauke da katunan zabe da aka samu sun lalace a kwalejin Rumfa da ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

  10. Wani ya ce ba zai yi zabe ba

    Abdullahi Musa mai sanaar faci a garin Bodinga da ke jihar Sokoto ya ce ba zai yi zabe ba.

  11. Mutane na kan layi tun kafin zuwan kayan zabe

    Masu kada kuri'a sun fito a Dutsen Alhaji da ke Abuja.Tun da sanyin safiya mutane suka hau layi.

  12. Sakon 'yan Najeriya mazauna Amurka

    'Yan Najeriya mazauna Amurka sun taya Najeriya murnar gudanar da manyan zabuka, inda suka yi addu'ar samun shugabanni na gari.

  13. Masu zabe sun yi layi a Abuja

    Masu zabe sun yi layi a birnin Abuja domin kada kuri'unsu a babban zaben Najeriya.

  14. Mazabar da Atiku zai yi zabe

    Mazabar Ajiya mai lamba 012 da ke Arewacin Yola, wurin da dan takarar shugaban kasa jam'iyar PDP, Atiku Abubakar.

  15. Labarai da dumi-dumi, Buhari da matarsa sun kada kuri'unsu

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai dakinsa Aisha Buhari sun kada kuri'unsu a mazabarsa da ke garin Daura na jihar Katsina.

  16. Kayan zabe sun isa mazabar Ajiya

    Wakilan hukumar zabe sun isa Ajiya Dan Nabara, mazabar Ajiya da ke Arewa cin Yola, jihar Adamawa..

  17. Mutane na jiran kayan zabe

    Masu kada kuri'a na jiran kayan zabe a rukunin gidaje da ke Shagari Quaters da Kundila a kwaryar birnin Kano.

  18. Ra'ayoyinku a shafinmu na Facebook

    Mun zabo wasu daga cikin ra'ayoyin da kuka bayyana game da zaben Najeriya a shafinmu na Facebook. Ga wasu daga cikinsu:

    Lawal S Zazzau Hakila yau ce ranar da mu 'yan Nigeria za mu kada kuri'unmu domin yanzu haka ma ni har na hau kan layi ina jira a kawo kayan zabe domin na jefa kuri'a ta ga wanda nake so.

    Abubakar Kawu Girgir Babu shakka mun shirya tsaf domin yanzu haka muna kan layin zabe domin yin tankade da rairaya a tsakanin 'yan takaarar da suka tsaya neman kujeru daban-daban.

    Jamilu Musa Sabonlayi Hakika rana ba ta karya domin haka na shirya tsaf domin fita kada kuri'a ta.

    Nura Lawali Danda Mu al'ummar jahar Zamfara mun shirya sosai domin kada kuri'unmu ga wanda muke so.

  19. Me ya sa mutane ke harkokinsu a Owerre?

    Masu hayar mota na ci gaba da harkokinsu a birnin Owerri da ke jihar Imo. Da alama neman kudi suka sanya a gaba ranar zabe.

  20. Labarai da dumi-dumi, Mutane na tsere wa daga Geidam

    Mutane da dama ne suke tsere wa daga Geidam na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sakamakon harbe-harebn da ake ji daga ko wanne bangare na garin. Bayanai sun ce manyan motoci sama da 200 ne dauke da mutane suka fice daga garin