Zaɓen Najeriya 2023: Kwamitin zaman lafiya ya yi kira da a kwantar da hankula

Shugaban kwamitin zaman lafiya na Najeriya, Abdulsalami Abubakar

Asalin hoton, Getty Images/Anadolu Agency

Bayanan hoto, Abdulsalami Abubakar
An wallafa

Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, inda ya ce tun bayan gudanar da zaɓe ranar Asabar sun sanya ido, inda ya ce duk da cewa an samu kura-kurai da 'yan matsaloli, amma zaɓukan sun gudana lami lafiya.

Ya ce a daidai lokacin da hankali ya karkata wajen jin sakamakon zaɓen, suna kira ga hukumar zaɓe da ta saurari korafe-korafen mutane wajen gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗi da tabbatar da an yi wa dukkan waɗanda suka fita suka yi zaɓe adalci.

Kwamitin ya ce ya samu rahotannin da suka nuna cewa an musguna wa wasu masu zaɓe a sassan ƙasar da dama ta hanyar tayar da rikici da hargitsa wajen kaɗa kuri'a da sayen kuri'a da kuma matsalolin da aka fuskanta da na'urar tantance masu zabe.

...
...

Tsohon shugaban ƙasar Najeriyar, ya ce yana kira ga dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa da cewa su ne za su ɗauki alhakin duk abin da masu magana da su suka faɗa, inda ya ce su guji furta kalaman da za su tayar da rikici ganin cewa sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar yin zaɓe lafiya.

Ya ce suna kira ga hukumar zaɓe ta tsaya wajen tabbatar da cewa sakamakon da za ta fitar ya zamanto sahihi wanda 'yan ƙasa za su yi na'am da shi.

Wannan kira na kwamitin zaman lafiya na zuwa ne bayan da manyan jam'iyyun adawa a zaɓeb shugaban Najeriya ke kokawa kan ingancin zaɓen.

Atiku Abubakar, Peter Obi, Kashim Shettima, Rabi'u Kwaknkwaso

Asalin hoton, Getty images/Anadolu Agency

Bayanan hoto, Atiku Abubakar, Peter Obi, Kashim Shettima, Rabi'u Kwaknkwaso

Jami'iyyar Labour Party, ɗaya daga jam'iyyun hamayya ta yi watsi da yadda ake tatttara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ake yi a Abuja.

Jam'iyyar ta ce ta yi watsi da sakamakon ne saboda INEC ta gaza wallafa sakamakon mazabu a shafinta na intanet a manhajar iREV kamar yadda ta yi alƙawari.

LP ta sa ayar tambaya kan sahihancin yadda ake karɓar sakamakon zaɓen da cibiyar tattara sakamako ta ƙasa da ke Abuja ke yi.

Su wane ne ke takarar shugabancin Najeriya?

Karin bayani kan 'yan takarar shugaban ƙasa na Najeriya

Zaɓi ɗan takara don ganin bayanansa

Bola Tinubu

All Progressives Congress (APC)

  • Shekaru: 70
  • Ya yi karatun akanta a jami'ar Chicago State University.
  • Gwamnan Jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007.
  • Ya wakilci Legas ta Kudu a Majalisar Dattijai daga 1992 zuwa 1993.
  • Gagarumin ɗan siyasa a Najeriya, wannan ne karon farko da yake yin takarar shugaban ƙasa.
  • Adawa da mulkin soja.
  • Ya ninka kuɗin shigar Jihar Legas na shekara-shekara sama da sau huɗu daga biliyan N22.2 a 1999 zuwa biliyan N220.9 a 2007.
  • Ya fara aiki a matsayin mai binciken kuɗi da kuma ma'aji a kamfanin Mobil Producing Nigeria, ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur mafiya girma a ƙasar.
  • Inganta harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa ƙasashen waje da kuma rage dogaro da sayen kaya daga waje.
  • Rage rabin adadi na rashin aikin yi tsakanin matasa cikin shekara huɗu da kuma ƙirƙirar ayyukan yi miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa cikin shekara biyu.
  • Gyara tsarin shari'a don mayar da hankali kan kare afkuwar laifuka da kuma inganta yarda kan jami'an tsaro.

Atiku Abubakar

Peoples Democratic Party (PDP)

  • Shekaru: 76
  • Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 - 2007.
  • Ya samu digiri na biyu a ɓangaren alaƙa tsakanin ƙasashe daga jami'ar Anglia Ruskin University da ke Ingila.
  • Tsohon jami'in kwastam ne wanda ya shiga siyasa a farkon shekarun 1980.
  • Sau biyar yana yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba; a 1993, 2007, 2011, 2015, da kuma 2019.
  • Ya kafa jami'ar American University of Nigeria, wadda ta bai wa 'yan matan Chibock tallafin karatu bayan Boko Haram ta sake su.
  • Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da jari a harkokin fetur da noma da bankuna da sashen haɗa magunguna.
  • Ƙudirin sayar da kadarorin gwamnati.
  • Bai wa 'yan kasuwa ƙarin dama wajen haɓaka tattalin arziki.
  • Inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar daidaito, da adalci tsakanin ƙabilun Najeriya.
  • Sauya tsarin tafiyar da gwamnati.

Peter Obi

Labour Party (LP)

  • Shekaru: 60
  • Gwamnan Jihar Anambra sau biyu daga 2007 zuwa 2014.
  • Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.
  • Ɗan kasuwa ne da ya karanta fannin falsafa a Jami'ar Najeriya, Nsukka.
  • Ya kafa wata gidauniya mai kuɗi dala miliyan 156 ƙunshe da kadarori ya zuwa lokacin da ya bar gwamnati.
  • Ya sauya Anambra daga matsayi na 26 zuwa na 1 a jerin jihohin da suka fi cin jarrabawar fita daga sakandare ta NECO da WAEC.
  • Ya mallaki harkokin hada-hada da suka samar da dubban ayyukan yi.
  • Tabbatar da sa ido a aikin gwamnati da kuma yaƙi da rashawa.
  • Mayar da Najeriya ƙasa mai sayarwa maimakon mai saye.
  • Fifita rayuwar ɗan Adam ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin-komai-da-ruwanka na STEM, da sashen lafiya, da kuma ayyukan raya ƙasa.

Rabiu Kwankwaso

New Nigeria Peoples Party (NNPP)

  • Shekaru: 66
  • Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007
  • Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
  • Ya wakilci Mazaɓar Madobi a Majalisar Wakilai a 1992 da kuma Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
  • Yana da digirin digirgir a injiniyanci daga jami'ar Sharda University da ke Indiya.
  • Ba da tallafin karatu da yunƙurin taimaka wa mutane.
  • Ƙara yawan ɗaliban firamare a 2011 daga miliyan ɗaya zuwa miliyan uku a 2015 lokacin da ya bar ofis.
  • Ya ƙaddamar da ciyar da ɗalibai 'yan firamare da ba su kayan makaranta kyauta.
  • Ya kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da kuma jami'ar Northwest, waɗanda su ne jami'o'in gwamnatin Kano kawai zuwa yanzu.
  • Samar da ayyuka ta hanyar zuba jari a ɓangaren noma.
  • Shawo kan matsalar tsaro.
  • Bin doka da ƙa'idar aiki.

Tun farko, wakilin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a wurin bayyana sakamakon zaɓen, Dino Melaye ya fice daga zauren da ake sanar da sakamakon.

Sai dai koken da ya fi jan hankali ya fito ne daga tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo, wanda ya buƙaci a soke sakamakon zaɓen wasu yankuna da aka samu hatsaniya.