Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya 2023: Kwamitin zaman lafiya ya yi kira da a kwantar da hankula
Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, inda ya ce tun bayan gudanar da zaɓe ranar Asabar sun sanya ido, inda ya ce duk da cewa an samu kura-kurai da 'yan matsaloli, amma zaɓukan sun gudana lami lafiya.
Ya ce a daidai lokacin da hankali ya karkata wajen jin sakamakon zaɓen, suna kira ga hukumar zaɓe da ta saurari korafe-korafen mutane wajen gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗi da tabbatar da an yi wa dukkan waɗanda suka fita suka yi zaɓe adalci.
Kwamitin ya ce ya samu rahotannin da suka nuna cewa an musguna wa wasu masu zaɓe a sassan ƙasar da dama ta hanyar tayar da rikici da hargitsa wajen kaɗa kuri'a da sayen kuri'a da kuma matsalolin da aka fuskanta da na'urar tantance masu zabe.
Tsohon shugaban ƙasar Najeriyar, ya ce yana kira ga dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa da cewa su ne za su ɗauki alhakin duk abin da masu magana da su suka faɗa, inda ya ce su guji furta kalaman da za su tayar da rikici ganin cewa sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar yin zaɓe lafiya.
Ya ce suna kira ga hukumar zaɓe ta tsaya wajen tabbatar da cewa sakamakon da za ta fitar ya zamanto sahihi wanda 'yan ƙasa za su yi na'am da shi.
Wannan kira na kwamitin zaman lafiya na zuwa ne bayan da manyan jam'iyyun adawa a zaɓeb shugaban Najeriya ke kokawa kan ingancin zaɓen.
Jami'iyyar Labour Party, ɗaya daga jam'iyyun hamayya ta yi watsi da yadda ake tatttara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ake yi a Abuja.
Jam'iyyar ta ce ta yi watsi da sakamakon ne saboda INEC ta gaza wallafa sakamakon mazabu a shafinta na intanet a manhajar iREV kamar yadda ta yi alƙawari.
LP ta sa ayar tambaya kan sahihancin yadda ake karɓar sakamakon zaɓen da cibiyar tattara sakamako ta ƙasa da ke Abuja ke yi.
Tun farko, wakilin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a wurin bayyana sakamakon zaɓen, Dino Melaye ya fice daga zauren da ake sanar da sakamakon.
Sai dai koken da ya fi jan hankali ya fito ne daga tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo, wanda ya buƙaci a soke sakamakon zaɓen wasu yankuna da aka samu hatsaniya.