'Yakin Ukraine zai iya daukar tsawon lokaci'

Jens Stoltenberg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Jens Stoltenberg ya ce dole ne a dage sosai a kan Ukraine
An wallafa

Shugabannin kasashen yammacin duniya na gargadin cewa yakin da ake yi a Ukraine ka iya daukar shekaru ana yinsa, kuma akwai bukatar tabbatar da ci gaba da ba kasar duk wani taimako da take bukata domin ta yi galaba a kan mamayar da Rasha ke yi mata.

Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Babban Sakataren kungiyar tsaro ta Nato Jens Stoltenbeg wanda yake cewa abin da yakin ke ci yana da girma gaya, amma kuma illar barin Rasha ta cimma burinta na soji ya fi hakan illa nesa ba kusa ba.

Shugaban na Nato ya ce, muddin ba a dage aka jure a kan hakan ba to kuwa ba shakka babu, shugaba Vladimir na Rasha zai mike kafa ne a kan burinsa sai abin da hali ya yi.

Mista Stoltenber, y ace dole ne a ci gaba da tallafa wa kasar ba kawai ta fannin soji ba har ma ta fannin farashin abinci da makamashi.

Haka shi ma firaministan Birtaniya Boris Johnson wanda ya ziyarci Kyiv a ranar Juma'a, ya yi irin wannan gargadi ne na cewa rikicin zai dauki tsawon lokaci.

Boris Johnson da Volodymyr Zelensky

Asalin hoton, BORIS JOHNSON

Bayanan hoto, Boris Johnson ya ce za su ci gaba da taimaka wa Ukraine da makamai da horo da kuma ta fannin tattalin arziki

Sannan ya bayyana wani shiri mai matakai guda hudu na samar da makamai da kuma tabbatar da taimaka wa Ukraine din ta fannin tattalin arziki yadda za ta iya jure wa yakin da Rasha.

Mista Jonson ya ce burin shugaban na Rasha ba zai tsaya ba, kawai wajen ganin ya wargaza Ukraine.

A jawabinsa na bidiyo na baya-bayan nan shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ba ta da isassun makamai masu linzami da za ta iya ganin bayan juriyar kasarsa.

A ci gaba da fafatawar da ake yi a yakin da safiyar Litinin an ji wata kara mai karfin gaske a babban birnin kasar ta Ukraine Kyiv, inda hukumomi suka ce wani abu ne mai shawagi na Rasha suka yi nasarar kakkabowa.

Mako biyu ke nan yanzu rabon da wani makami mai linzami na Rasha ya fada wa babban birnin, yayin da Rashar ta bayar da karfi a yakin a banagaren gabashin kasar.