Martanin da ya biyo bayan yunƙurin Ganduje na karɓo bashin biliyan 10

Gwamna Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, Kano State Government

Bayanan hoto, Gwamnatin Ganduje ta ce kuɗin ruwan da za a biya na bashin bai kai kashi 10 cikin 100 ba
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, mazauna jihar da wajenta na mayar da martani game da yunƙurin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karɓo bashin naira biliyan 10 don inganta harkokin tsaro a jihar.

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Kano ta amince da buƙatar gwamnatin jihar ta ciyo bashin don sayen kayayyakin inganta tsaro da suka haɗa da kamar kyamarar CCTV.

"Daga cikin abubuwan da za a saya har da kyamarar tsaro ta CCTV da kuma gina ɗakunan ɗaukar bayanai ta yadda jami'an tsaro za su gudanar da ayyukansu cikin nasara," kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa Labaran Abdu Madari ya shaida wa BBC Hausa.

Cikin martanin da suka yi game da ciyo bashin, ƙungiyoyin farar-hula a Kano sun yi zargin cewa a baya ma an karɓi irin wannan bashin da sunan inganta harkar ilimi, da samar da manyan motocin sufuri amma ba a gani a ƙasa ba.

Sai dai magoya bayan gwamnatin Ganduje na kare matakin da cewa "kafin ku zargi Ganduje, ga ɗaya daga cikin gadojin da ya gina a Kano kuma ba ta cikin ukun farko na ire-irenta", a cewar wani mai suna Mohammed Shehu a shafinsa na Facebook.

Kauce wa Facebook, 1

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

Bayanan bidiyo, Manyan dalilan da suka sanya na fita daga APC zuwa NNPP - Shekarau

'Akwai abubuwan da gwamnati ya kamata ta mayar da hankali a kansu'

Da take martani, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin gwagwarmaya a Kano Barista Maryam Abubakar ta ce babu dalilin da gwamnatin za ta ciyo wannan bashi saboda akwai wasu abubuwa da gwamnati ya kamata ta mayar da hankali.

"Za a iya magance matsalar tsaro ta wasu ɓangarorin kamar samar wa al'ummar Kano ayyukan yi, idan aka yi haka zai rage yawan waɗanda ba su da aikin yi a garin nan," a cewar lauyar.

Ta ƙara da cewa: "Babu dalilin da ya sa za a ciyo wannan bashi, saboda akwai basussuka da gwamnatin ta ciyo kuma har yanzu ana batun yadda za a biya su.

"Akwai abubuwa da dama da su ne suka addabar al'umma waɗanda kuma gwamnatin ya kamata ta fi mayar da hankali a kansu."

Wannan layi ne

A ina za a karɓo bashin?

Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya faɗa wa BBC Hausa cewa gwamnatinsu za ta karɓo bashin ne daga bankin Accces Bank.

"Su ma bankin Acccess ɗin sun ga muhimmancin abin, shi ya sa ma suka rage mana kuɗin ruwa da za a biya, inda suka rage shi zuwa ƙasa da kashi 10 cikin 100," in ji shi.

"Wannan gwamnati na taka-tsantsan da duk bashin da za ta karɓa; sai ta tabbatar yana da amfani ga al'umma. Sannan kuma mai binciken kuɗi na gwamnati zai yi bibiya ya ga an yi amfani da su ta hanyar da ta dace."

Wannan layi ne

Abin da Kanawa ke cewa

Mazauna Kano da wajenta na bayyana ra'ayoyi daban-ddaban game da mauƙudan kuɗin, musamman a shafukan sada zumunta.

Wani da ya kira kansa Bakano ya ce labarin ya ja hankalinsa kuma ya yi ira ga gwamnatin Ganduje ta duba sauran yankunan karkara.

Ra'ayin Shamsi

Asalin hoton, Facebook

Shi ma wani mai suna Ibrahim Musa ya yi gugar-zana game da bashin, yana mai cewa "za a karɓo bashi daga bankin da ke karɓar kuɗin ruwa".

Kauce wa Facebook, 2

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2

Kazalika, Nuhu Adam ya nemi 'yan majalisar ta Kano "su dinga yin karatun ta-nutsu kafin amincewa da irin waɗannan basussuka".

Ra'ayin Nuhu

Asalin hoton, Facebook

Wannan layi ne