Muhawarar da ake yi kan zaɓar Yusuf Gawuna ya gaji Ganduje a Kano

Asalin hoton, Kano State Government
Tabbatar da goyon baya da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi ga mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda yake so ya gaje shi a hukumance ya sa Kanawa da masu sha'awar siyasa ɗorawa daga inda suka tsaya a muhawararsu.
A ranar Talata ne Ganduje ya miƙa wa Gawuna fom ɗin takarar gwamna tare da Muratala Sule Garo, tsohon kwamashinan ƙananan hukumomi wanda ake wa laƙabi da kwamanda, a matsayin abokin takararsa yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin na Kano.
Sai dai tun a ƙarshen mako gwamnan ya amince Gawuna ya maye gurbinsa sannan majalisar masu ruwa da tsakin ta amince Ganduje ya tsaya takarar sanata a yankin Kano ta arewa.
Kamar yadda aka saba a siyasar Kano da ma saura, jam'iyyar APC mai mulkin Kano na cikin rikici sannan ta afka cikin wani sabo jim kaɗan bayan zaɓen Gawuna da Murtala.
Goyon baya da adawa

Asalin hoton, KNSG
Dubban mutane suka dinga tafka muhawara tun bayan ɓullar labarin a ƙarshen makon da ya gabata.
Mutum fiye da 3,500 ne suka yi tsokaci kan labarin da BBC Hausa ta wallafa a dandalin Facebook, yayin da mutum kusan 100 suka yi martani a Twitter, kuma akasarinsu na goyon bayan ne da kuma adawa da 'yan takarar.
"Muna sane da satar akwatin xa6e da yaga takardun kaɗa ƙuri'a da suka yi a mazaɓar Gama," a cewar Umar Ado Tahir.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Amma Rabiu Uba goyon bayan Gawuna da Garo yake, yana mai cewa "a yi Gawuna da alkairi".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Ra'ayin Mahmud Salihu kuwa ma na rashin goyon baya ne.

Asalin hoton, Facebook
Rabiu Nuhu kuma addu'a ya yi wa Kanawan addu'a ta zaɓin alkairi.

Asalin hoton, Facebook

Na rantse da Allah za mu yi tafiya irin wadda Ganduje yake so - Nasiru Gawuna

Asalin hoton, Facebook/Nasiru Yusuf Gawuna
Da yake martani jim kaɗan bayan ƙaddamar musu da fom ɗin takarar, Nasiru Yusuf Gawuna ya gode wa Ganduje tare da yin rantsuwa da Allah cewa za su riƙe amanar gwamnan.
"Billahil lazi la ilaha illahuwa mai girma gwamna za mu riƙe maka amanarka, za mu yi tafiya irin wadda kake so," a cewarsa. "Kuma bi izinillahi kai ma Allah zai cika maka buƙatarka."
Mataimakin gwamnan ya ƙara da roƙon 'ya'yan jam'yyarsu da ka da wanda ya munafinci ko cin amana.
"Ina roƙon 'yan jam'iyyarmu da muka haɗu a nan, na haɗa ku da girma Allah yadda mai girma gwamna ya haɗa ni da ɗan uwana - shi ya san amanar da ke tsakanina da shi - don Allah don Annabi ka da wanda ya kawo mana annamimanci."

Tasirin Gawuna da Garo a siyasar Ganduje

Asalin hoton, Other
Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna da kuma Kwamashinan Ƙananan Hukumomi Murtala Sule Garo sun taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2019, lokacin da Gwamna Ganduje ke neman wa'adi na biyu.
Kasancewarsu na gaba-gaba a harkokin zaɓen tasa har sai da 'yan sanda suka kama mutanen biyu yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen da aka gudanar zagaye na biyu a unguwar Gama da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano a zaɓukan 2019.
Wani hoto da ya karaɗe shafukan zumunta a lokacin ya nuna Murtala na tafiya da saɓulallen wando a lokacin yayin da suke fafutikar yi wa jam'iyyarsu ta APC aiki.
Wannan ta sa aka fara yi masa laƙabi da kwamanda a siyasar Kano.

Asalin hoton, KNSG









