Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutanen da ya kamata su bayar da gudunmawar jini da waɗanda bai dace su bayar ba
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta buƙaci mutane a faɗin duniya su bayar da gudunmawar jini a matsayin wata hanyar nuna haɗin kai da goyon baya.
Hukumar na wannan kiran ne albarkacin Ranar Ba Da Gudunmawar Jini ta Duniya wadda ake gudanarwa a duk ranar 14 ga watan Yuni.
Buƙatar Jini dai iri ɗaya ce a ko ina cikin duniya, amma yana da iyaka musamman a ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin samu, inda lamarin ya fi illa ga mata da ƙananan yara, don kuwa su ne suka fi tsananin buƙatar jinin.
BBC ta ji ta bakin wasu 'yan Najeriya, inda ta tambaye su ko sun san muhimmancin ba da gudunmawar jini?
Usman Zamfara daga ƙaramar hukumar Birnin Magaji ya ce "gaskiya ni ban san muhimmancin ba, amma masu niyyar yi Allah Ya taimake su Ya ba da sa'a.
"Ina da maleriya da taifod da atini kuma shekara 60, ka ko ga ai jinina ya yi nisa."
Sai dai mutumin ya ce ya san muhimmancin bayar da jinin, "domin taimako ne ga wanda ba shi da lafiya kuma kowa na son a taimake shi," ya ce.
Salisu Badamasi daga jihar Katsina cewa ya yi ya san muhimmancin bayar da jini sosai, kuma yana shirin bayar da gudunmowar jinin.
"Na yarda cewa bayar da jini taimako ne baki ɗaya, duk da dai ba a taɓa ƙaramin jinin ba amma na sha bayarwa ko kwanan nan an dibar min, na bayar."
Shi ma Hassan Wanzam ya ce ya sha bayar da gudunmowar jini, "kusan duk shekara idan na je garinmu zan ji ana neman taimakon jini kuma ina zuwa na bayar.
Ya ƙara da cewa ya bayar da jini ya kai sau bakwai. Sai dai ya ce bai san akwai rana ta musamman ta bayar da jinin ba, amma ya bayyana hakan a matsayin gagarumin lamari na wayar da kan al'umma.
Sani Muhammad Goga kuwa cewa ya yi sau ɗaya ya ta ba bayar da jini tun skhekarar 1982 a lokacin yana ɗalibin jami'a, kuma ya ce shi ma an taɓa ƙara masa jinin amma ba kyauta aka ba shi ba, saya ya yi.
Sai dai dukkan mutanen sun yi kira ga ƴan ƙasa da su dinga bayar da gudumowar jini, sanna suka ce ya kamata ita ma gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen kula da lafiyar mutane.
Wasu labaran da za ku so ku karanta
A Kamaru
A maƙwabciyar Najeriya Kamaru kuwa, ƙasar ta zamo ɗaya daga cikin kasashe 79 a jerin kasashe masu tasowa da WHO ta ce suna fuskantar karancin masu bayar da jininsu a kyauta.
Alkaluma sun nuna cewa kasa da mutum 10 ne cikin 1,000 suke iya bayar da jininsu ga marasa lafiya.
Alhalin kuma ana bukatar robobin jinni 400,000 a kowace shekara domin ceto rayukan marasa lafiya da suke da bukata. Sai aka wayi gari kawai robobi 103,000 ake samu da ƙyar.
Lamarin da ya sa ake ta ruɓanya kira ga jama'a da su kai ɗauki.
Wane ne zai iya bayar da jini?
Tambaya mai muhimmanci a nan ita ce wane ne zai iya bayar da gudunmowar jini?
Hukumar Inshorar Lafiya ta Birtaniya NHS ta ce akwai abubuwan da kake buƙatar su kafin ka bayar da jini:
- Dole ya kasance lafiyarka ƙalau babu wata cuta da ke damunka
- Shekarunka su kasance daga tsakanin 17 zuwa 65
- Dole nauyinka ya kasance daga kilogiram 50 zuwa kilogiram 158
- Dole a duba ko jijiyoyinka suna da lafiya da sauƙin ɗibar jinin yadda ake so
- Sannan dole sai an duba ko jinin naka lafiyayye ne ba ka ɗauke da wata cuta (ana yin wannan kafin a ɗebi jinin ne).
Waye ba zai iya bayar da jini ba?
Ba za ka iya bayara da jini ba idan har kana da abubuwan da za a zayyano a ƙasa:
- Idan kana da wani nau'i na cutar daji wato kansa
- idan kana da wata matsala da ta shafi zuciya
- idan har an taɓa yi maka ƙarin jini tun bayan ranar 1 ga watan Janairun 1980
- idan kana da cutar HIV ko Aids
- idan an taɓa yi maka dashe na ƙoda ko wani abu daban
- idan kana da cutar hanta ta hepatitis B
- ko idan kana da cutar hanta nau'in hepatitis C
- idan ka taɓa yin allura ko shan magani wanda ba likita ne ya rubuta maka ba musamman irin na gina jiki ko masu ɗauke da sinadaran jimar fata. Amma kana iya bayarwa idan har likita ne ya rubuta maka labarin da kansa.
Sannan akwai sauran yanayi na rashin lafiya da ke nufin ba za ka iya bayar da jinin ba.
Akwai kuma wasu dalilai na lafiya ko tafiye-tafiye da salon rayuwa da ka iya dakatar da kai na ɗan lokaci wajen bayar da kyautar jini.
Amma hukumar NHS ta jadda cewa abu mafi kyau shi ne mutum ya je asibiti don a tabbatar da zai iya bayarwa ko bai zai iya ba.
Abin da ya shafi jima'i
- Dole ne sai ka jira tsawon wata uku kafin ka bayar da jini idan har:
- an sadu ta dubura a wata ukun da suka gabata.
- idan har ka sha magungunan kariya daga kamuwa da cutar HIV bayan tsammanin ko ka yi mu'amala da mai cutar a wata uku da suka gabata.
- idan ka yi mu'amala a wata ukun da suka gabata da mai cutar HIV ko mai ciwon hanta nau'in hepatitis B da nau'in hepatitis C ko mai ƙaba.
Sannan kuma mutum ba zai iya bayar da jini ba idan har ba shi da lafiya ko mai ciki ko mai shayarwa ko kuma wanda aka yi wa shasshawa ko ɓula kunne.
Mata ƴan ƙasa da shekara 20
Idan ke mace ce kuma ƴar ƙasa da shekara 20 kuma nauyinki bai kai kilogirma 65 sannan tsawonki bai kai santimita 168 ba, to dole sai kin duba yawan jinin da kike da shi kafin ki bayar da gudunmowarsa.
Kina iya duba yawan jinin ne ta hanyar zuwa asibiti a auna miki.
Za a iya bayar da jini a kai - a kai?
Maza na iya bayar da jini duk bayan mako 12 yayyin da mata kuma za su iya hakan ne bayan mako 16 kawai.
Abin da ya sa hakan kuma shi ne saboda sinadarin ayon ɗin da ke jikin maza ya fi na jikin mata yawa.