Ana kaɗa ƙuri'a a Armenia kan zaɓin ƙulla alaƙa da turai ko Rasha
Mutanen Armenia na kaɗa ƙuri'a a majalisar ƙasar domin tantancewa ko ƙasar za ta cigaba da kasance tana da alaƙa ne da turai ko kuma ta fi ƙulla alaƙa da Rasha.
Jam'iyyar Firaministan ƙasar Nikol Pashinyan ta fi karkata kan ƙara ƙulla alaƙa da tarayyar turai, kuma ana tunanin ita ce za ta samu rinjaye a ƙuri'ar, duk da cewa ba ta da tabbacin samun gagarumin rinjaye.
Babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar kuma, wadda take ƙarƙashin jagorancin fitaccen ɗankasuwa Samvel Karapetyan, wanda ke zaune a Rasha tana son akasin haka.
Rasha dai ta ƙaƙaba wa Armenia takunkumin tattalin arziki, sannan shugaban na Rasha Vladimir Putin ya nanata cewa zai ƙara lafta mata wasu takunkumin idan ƙasar ta cigaba da raɓar turai