Ranar ma'aikatan jinya ta duniya: ‘Na yi aiki lokacin cutar HIV, Ebola da Korona’

    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

"Har yanzu ina raye, ina kuma ci gaba da aiki. Ina farin ciki da hakan, ganin na samu damar yin aiki da ceton rayukan al'umma," in ji malamar jinya Sylvia Jabbie, cikin wani yanayi na ba yabo ba fallasa.

"Ina daga cikin jami'an lafiya sahun farko a kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki, da annobar Ebola da Korona. Yawancin mutane na yaba wa aikina,"in ji Haurace Nyandemoh.

Wadannan mutane biyun, na daga cikin wata karamar kungiyar ma'aikatan jinya a kasar Saliyo da ke yammacin Afirka, wadanda suka kula da majinyatan da ake fama da cutar HIV mai karya garkuwar jiki, da lokacin barkewar cutar Ebola da annobar Korona da ta shafi daukacin duniya.

A ranar ma'aikatan jinya ta duniya, matan biyu Sylvia da Haurace sun shaida wa BBC tashin hankali da mawuyacin halin da suka shiga a matsayin su na jami'an lafiya da ke sahun gaba a yaki da cutukan.

Cuta mai karya garkuwar jiki

Sylvia Jabbie ta na aiki ne a Lunsar da ke arewa maso yammacin kasar Saliyo - a yanzu ta fi aiki a dakin karbar haihuwa, tana kuma kula da matan da suke haihuwa musamman ta hanyar tiyata.

Idan ta yi waiwaye a shekarar 2002, lokacin tana aiki a babban asibiti da ke birnin Freetown, an bukaci ta kula da wata matashiya mai shekara 22 da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki wato Aids.

Aiki ne mai matukar wuya: a wancan lokacin ana matukar kyamar masu cutar Aids.

"Mutane na kallo na a shekeke. Yawanci sun gargade ni na kiyaye kada na dauki cutar. Jikina ya mutu murus, wasu lokutan na kan yi tunanin ko dai ina da cutar da kai na a wannan aikin."

Duk da wannan damuwar, ta ci gaba da aikinta. Sylvia na aikin kula da mutane a gida, yi mata wanka, sauya mata tufafi, da sharce gashi, da taya ta hira.

"Wata rana, maras lafiyar ta tambaye ni ko za ta warke."

Lamari ne mai karya zuciya. Sylvia ta shaida wa mara lafiyar, garkuwar jikinta ta gaza, wasu sassan jikinta kamar hanta za su dakatar da aiki a kowanne lokaci.

Abin da Sylvia ta iya mata alkawari shi ne za ta taimaka mata samun sassaucin radadin ciwo.

"Mun dauki mintina shiru. Sai maras lafiyar ta ce min, 'Na san mutuwa zan yi, gara mutuwa da irin halin da na ke ciki.'"

"Sai ta sanya min albarka, tare da yi min addu'a."

A wannan lokacin babu isassun magungunan da za a bai wa masu cutar Aids a Saliyo, don haka Sylvia, ta dogara da dan abin da suke samu na tallafi daga asibiti. Ta shafe kwanaki 51 ta na jinyar matar.

"Ta mutu lokacin da ta sarkafe hannunta cikin nawa. Ban yi kuka ba lokacin da ta rasu. Duk da cewa ina tsammanin hakan," kamar yadda Sylvia ta tuna.

Cuta mai karya garkuwar jiki ta yi ajalin mutum miliyan 36 tun barkewarta a duniya a shekarun 1980, kamar yadda Hukumar Lafiyar ta Duniya ta duniya ta bayyana.

Ashekarar 2020, kusan mutum 680,000 cutuka masu alaka da AIDS suka yi ajali a fadin duniya. Saliyo na da mutum 3200 a cikin mamatan.

An bai wa Haurace Nyandemoh aikin kula da kwantar wa masu cutar HiV hankali a shekarar 2017.

"Yawancin matan matasa ne 'yan shekara 20. Ana ba su magungunan da suka shafi karfafa garkuwar jiki,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Daya daga cikinsu ma ta rasu shekara daya baya. Ana ba su maganin kashe kaifin ciwon," ya fada a hirarsa da BBC.

Dukkan marasa lafiyar da yake kula da su, suna samun sauki. Hasali ma ya ce mutum guda kadai ya mutu, kimamin shekara guda kenan.

Godiya ga ci gaban da aka samu na magungunan cutar, da kwararrun jami'an lafiya, da kirkirar shirin lafiya da shigar kungiyoyi masu zaman kansu wajen ba da tallafin magunguna a kasashe matalauta, har da kokarin gwamnatoci na kula da masu cutar ta HIV.

"A yanzu ana samun masu cutar HIV da ke gudanar da rayuwarsu cikin walwala. Suna da aikin yi, wasu ma aikin gwamnati da sauran su, ko a fuska ba za ka taba cewa suna fama da wata cuta ba bare kuma HIV," in ji Haurace.

Ebola

Daga Sylvia har Haurace na da mummunan abin da ya faru da su lokacin barkewar cutar Ebola.

An fara gano cutar Ebola ne a shekarar 1976, bayan wannan lokacin sai ta sake bayyana. Barkewa ta baya-bayan nan a kasar Saliyo ne a shekarar 2014, kimanin shekara biyu bayan barnar da cutar amai da gudawa ta yi, da ta hadassa mutuwar kusan mutane 400 a kasar.

"Alamomin cutar kwalara sun hada da amai da gudawa. Su ma masu cutar Ebola na da alamomi kamar kwalara lamarin da ke ta matukar sarkakiya," in ji Haurace.

Mace-macen da annobar Ebola ta haddasa, ta haddasa tsoro da fargaba a zukatan mutane. Sai kuma kullaliyar da aka kulla wa jami'an lafiya da cewa su ne suka yada cutar.

"Yadda jama'a suka dauki lamarin na daga cikin abin da ya kara dagula lamura. Wasu kauyawa kan kai wa motocin jami'an lafiya wadanda aka turo su dauki marasa lafiya," in ji Sylvia.

Cikin daya daga hari mafi muni da aka kai wa jami'an lafiya, an kashe takwas daga cikin tawagar jami'an lafiya da suka je kauyuka domin wayar da kai kan cutar ta Ebola, kauyawan suka far musu da sara da suka da adduna a makwafciyar Saliyo wato Guinea a watan Satumbar 2014.

An kai matakin da sai an hada da jami'an 'yan sanda domin ba su kariya kafin su binne gawa, haka kuma hatta asibitocin da ake killace masu cutar.

A birin Freetown, baya ga kamarantar da horas da 'yan sanda da aka maida wurin killace masu cutar Ebola, an kuma sake ware wasu asibitocin. Haurace Nyandemoh ya kadu matuka kan abin da ya gani a can.

"Mutane da dama na ta mutuwa. Wata ranar Lahadi marasa lafiya 48 ne suka mutu a cibiyar. Lamarin mai tada hankali ne."

Shida daga cikin abokan aikin Haurace sun mutu sanadiyar Ebola. Wasu malaman jinya sun tsere saboda tsoro sun gwammace su ajiye aikin, amma duk da hakan Haurace bai karaya ba, ya ci gaba da aiki.

''Akwai kaduwa matuka. Babu wanda ke son kula da marasa lafiyar. Ina sanya safar kariya ta hannu guda shida, kafin shiga inda masu cutar ebola suke. A gida kuwa, killace kai na nake yi, ba na taba yadda mu hadu da matata ko da na."

Haurace ya shiga matsananciyar damuwa da tsoro, lokacin da dan shi ya fara rashin lafiya.

"A firgice nake, na gagara daukar shi zuwa asibiti domin a yi masa gwaji."

Ashe ba Ebola ba ce, kwanaki kadan yaron ya samu lafiya.

Da gangan Sylvia ta daina zuwa wajen aiki. Amma rokon da abokan aikinta ke yi ya sanya dole ta koma bakin aiki.

"Na sanya rigar kariya, aka kuma fesa min maganin kashe kwayoyin cuta."

Sinadarin Chlorine da aka fesa wa kayan jikinta na kariyar, ya sanya ta shiga mawuyacin hali, cikin jikinta tana jin wani matsanancin zafi saboda rashin sabo da rigar kariyar.

Da kyar ta ke magana.

"An shaida mana kada mu je kusa da marasa lafiyar. Yawancinsu na cikin mawuyacin hali. Sun fita daga hayyacinsu, sannan dakyar suke iya magana."

A kowacce rana, akalla mutum biyar zuwa 10 na mutuwa a dakin da take kula da su. Ebola ta kashe jami'an lafiya 12 ciki har da likita daya da malaman jinya takwas a asibitin da take aiki.

"A ɗarare na ke, kullum ina fadawa kai na, ya kamata na jajirce a aikin nan saboda nan ce makarfafata."

Babu maganin cutar Ebola, amma likitoci na amfani da magungunan cutar malaria da masu dauke da sinadarin zinc domin karfafa garkuwar jikinsu.

"Ba kamar yadda aka saba ba. Da safe na tunkari marasa lafiya dauke da murmushi a fuskata, tare da tambayar karfin jikinsu. A kan hanyar komawa gida, ina yawan tunawa da mara lafiyar da ya mutu a lokacin da nake bakin aiki."

Idan lafiyar wasu ta inganta, suka fara magana, Sylvia ta kan ba su wayar tarho.

"Su dinga hira da 'yan uwansu, wannan na sanya su suna samun sauki cikin sauri," in ji ta.

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Amurka, ta ce cutar Ebola ta kama mutum 28,616 da hallaka mutum 11,310 a kasashen Guinea, Laberiya, da Saliyo tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016. An kuma sake samun wasu 36 da suka kamu da 15 da suka mutu a wasu kasashe uku.

Korona

Ana tsaka da jin dadi sai kuma aka fara yada jita-jitar bullowar wata sabuwar cutar. Haurace ta tuna lokacin da mambobinsu ke cewa a lokacin da aka samu batun barkewar annoba, "sabuwar cutar ba za ta yi wa bakaken fata 'yan Afirka."

Ranar 30 ga watan Maris 2020, cutar Korona ta isa kasar Saliyo, dalilin wani matafiyi.

Cibiyoyin da aka kafa na yaki da cutar Ebola, kamar wuraren killace marasa lafiya sun yi amfani lokacin da cutar Korona ta bulla a kasar Saliyo.

Wani abin birgewa shi ne, Korona ba ta yi wa Saliyo mugun duka ba. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana mutum 125 ne korona ta kashe a kasar.

"Mutane sun fahimci hadarin da suke ciki da fahimtar halin da duniya ke ciki, suna bai wa jami'an lafiya hadin kai saboda karonsu da Ebola bai yi dadi ba. Don haka bin dokoki lokacin korona bai zo da wuya ba," in ji Sylvia.

WHO ta ce kusan mutum miliyan 15 ne korona ta hallaka a fadin duniya baki daya, wannan adadi ya rubanya sau biyu idan aka kwatanta da kididdigar da ba ta hukuma ba.

Aiki lokacin barkewar annoba har biyu, da cuta mai yaduwa sun sauya rayuwar dukkan malaman jinyar.

Sylvia ta kara jin dadi da alfaharin abin da ta karanta, wanda shi ne burinta tun tana karama, duk a cewa an fuskanci kalubale da dama. Sylvia mai 'ya'ya biyu, ta ce ta na jin kwarin gwiwa, da fatan ''mummunar annobar ta korona ta yi sallama da duniya."

Haurace ma kyakkyawan fatan gare shi: "Yanzu mun san abin da barkewar annobar da yadda ta ke da makomarmu ta ke, za kuma mu samu kwarin gwiwa idan wata annobar ta sake barkewa.''