Tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey, yana cikin ƴan wasa tawagar Ghana Ghana da za ta halarci gasar Kofin Duniya a bana.
Partey ya musanta laifuka guda bakwai na yi wa mata fyade da kuma ɗaya na cin zarafi, da ake zarginsa da aikatawa tsakanin 2020 zuwa 2022, dangane da korafe-korafe daga mata huɗu daban-daban.
Ɗan wasan mai shekara 32, wanda yanzu ke buga wa Villarreal tamaula a La Liga, zai gurfana a gaban kotu a shekara mai zuwa.
Partey ya buga wa Arsenal wasa 167 a dukkan fafatawa tsakanin 2020 zuwa 2025, amma ya bar Emirates a bazarar da ta gabata bayan kwantiraginsa ya ƙare.
Kocin Ghana, Carlos Queiroz, ya saka Partey cikin jerin ƴan wasa 28 na wucin gadi domin atisaye kafin Kofin Duniya da kuma wasan sada zumunci da Wales a Cardiff a ranar 2 ga Yuni.
Partey ya ci gaba da kasancewa cikin tawagar yayin da Queiroz ya cire masu tsaron raga Solomon Agbasi da Paul Reverson domin rage adadin zuwa ƴan wasa 26 na ƙarshe.
An cire mai tsaron baya Alexander Djiku bayan da ya ji rauni a yayin da Spartak Moscow ta lashe kofin Russia, don haka aka maye gurbinsa da Derrick Luckassen, wanda aka haifa a Netherlands kuma ya fara buga wa Ghana tamaula a watan Maris.
Haka kuma akwai Antoine Semenyo na Manchester City da Brandon Thomas-Asante na Coventry, tare da ƴan wasan Leicester Jordan Ayew da Abdul Fatawu.
Joseph Anang, wanda ke buga wa St Patrick Athletic a League of Ireland, yana ɗaya daga cikin masu tsaron raga uku a tawagar.
Mai taka leda a Tottenham, Mohammed Kudus bai samu goron gayyata ba, saboda raunin ƙafa da ya hana shi buga wasa tun watan Janairu.
Jerin ƴan wasa 28 da Ghana ta bayyana:
Masu tsaron raga: Benjamin Asare (Accra Hearts of Oak SC), Lawrence Ati-Zigi (St Gallen), Joseph Anang (St Patrick's Athletic).
Masu tsaron baya: Baba Abdul Rahman (PAOK), Gideon Mensah (Auxerre), Marvin Senaya (Auxerre), Alidu Seidu (Rennes), Abdul Mumin (Rayo Vallecano), Jerome Opoku (Istanbul Basaksehir), Jonas Adjetey (Wolfsburg), Kojo Oppong Peprah (Nice), Elisha Owusu (Auxerre), Derrick Luckassen (Pafos).
Masu buga tsakiya: Thomas Partey (Villarreal), Kwasi Sibo (Real Oviedo), Augustine Boakye (Saint-Etienne), Caleb Yirenkyi (Nordsjaelland), Abdul Fatawu Issahaku (Leicester City).
Masu cin ƙwallaye: Kamaldeen Sulemana (Atalanta), Christopher Bonsu Baah (Al Qadsiah), Ernest Nuamah (Lyon), Antoine Semenyo (Manchester City), Brandon Thomas-Asante (Coventry City), Prince Kwabena Adu (Viktoria Plzen), Inaki Williams (Athletic Bilbao), Jordan Ayew (Leicester City).