Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴan bindigan da suka sace mata da ƴaƴan sarki suka nemi Naira miliyan 100
Wasu 'yan bindiga sun kai samame rugar sarkin Fulani da ke gefen garin Lafiyagi, shalkwatar karamar hukumar Edun ta jihar Kwara, inda suka sace dan sarkin Fulanin da matansa biyu masu dauke da goyon jarirai, ciki har da jaririn da bai kai wata guda da haihuwa ba.
Sun kuma kashe wani mutumin garin, suka tafi da dansa shi ma.
Maharan suna neman a ba su naira miliyan dari a matsayin kudin fansa, kafin su sako mutanen da suka sace.
Al'amarin da ke kara nuna matsalar hare-haren 'yan bindiga dai ba ta bar hatta Fulani makiyaya da ke daji ba.
A cewar Ali Muhammadu Janwuro, shugaban reshen jihar Kwara na kungiyar Fulani makiyaya ta Mi-Yetti-Allah Pulako Yeso-Yeso, yan bindigar sun kai harin ne da tsakar dare, inda barayin suka dauki matan biyu suka wuce da su, sai ranar Laraba suka sake dawowoa suka sake tafiya da wasu.
Ya ce suna zargin cewa 'yan fashin daji da suka addabi jihar ne suka kai wannan hari na baya bayan nan.
Ya kara da cewa yan fashin dajin sun kira mutane sun shaida masu cewa ba za su cutar da mutanen ba, sai dai dole za a biya su Naira miliyan 100 kafin su sake su.
''Sun ce a je a ba su Naira miliyan 100, shi kuma sai ya ce musu ba shi da wannan kudi, yanzu dai babu wani karin bayani, don haka suna ci gaba da rike mutanen da suka sace su'' inji shi.
Sai dai Honarabul Sa'idu Baba Ahmed, shugaban kwamitin kananan hukumomi da masarautu na majalisar dokokin jihar Kwara, kuma daya daga cikin shugabannin al'ummar Fulani a jihar, ya ce ana bin sawun wannan batu.
Reshen kungiyar Fulanin makiyaya ta Mi-Yetti-Allah Pulako Yeso-Yeso na jihar ta Kwara, ya ce an kwashe shekara takwas jama'arsu suna fama da wannan matsala ta tsaro, wadda ya zuwa yanzu ta yi sanadin sace makiyaya da dama, da haddasa masu asarar dabbobi fiye da dubu biyu a yankin karamar hukumar ta Edu. Al'amarin da suke kukan ya zame masu gaba kura baya siyaki.
Najeriya na cigaba da fuskantar matsalolin hare-hare a sanadiyar matsalar tsaro da ta yi wa ƙasar dabaibayi, musamman a yankin arewaci.
Sannan ƙungiyoyin ƴanbindiga sun fi ƙarfi a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Akwai ƙungiyoyin mahara sama da 100 da suke aika-aikar, kamar kai hare-hare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sauransu.
Masana sun ce ƙungiyoyin suna ƙara samun ƙarfi ne saboda talauci da rashin aikin yi, sannan sun fara ne da satar shanu da ƙananan rikice-rikice, kafin ayyukansu suka ta'azzara tare da faɗaɗa.