Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karancin likitocin tiyata na jefa al'ummar Nijar cikin tasku
A jihar Maraɗin Jamhuriyar Nijar, wata matsala da ke ci wa al'umma tuwo a ƙwarya ita ce ta rashin isassun likitoci musamman masu yin allurar barci lokacin tiyata.
Gomman mutane ne dai ke can babban asibitin jihar, suna jiran aiki bayan cikar wa'adin da likitocin suka ba su.
Matsalar ta haifar da kwararar masu jinyar marasa lafiya kan tituna, don barar abin da za su ci da sauran buƙatun rayuwa.
Kwaliyar BBC a Nijar, Tchima Illa Issufou, ta yi tattaki zuwa babban asibitin jihar ta Maradi inda ta gaba tare da tattaunwa da wasu daga cikin marassa lafiya da kuma iyayen yaran da ke jiran a yi wa 'ya'yansu tiyata tsawon lokaci.
Wakiliyar ta BBC, ta ce akwai yara sama da dari da biyu a asibitin da ke jiran a yi musu tiyata.
Masu jinyar yaran na cikin halin damuwa ta yadda duk wanda ka kalla za ka ga alamun bakin ciki a tare da shi in ji wakiliyar ta BBC.
Daya daga cikin iyayen wadannan yaran da BBC ta tattauna da shi Malam Bara'u ya ce ya shafe sama da kwana 25 yana kai komo tsakanin garinsu da kuma asibitin a kan lalurar da 'yarsa ke fama da ita.
Ya ce,"Yarinya ce na kawo aka yi mata tiyatar farko na ke so a yi mata ta biyun kamar yadda likitoci suka fada, yanzu mun mun kusa shafe wata muna zaryar a gyara wa yarinyar tiyatar da aka yi domin ta samu lafiya amma abin ya ci tura."
Ya ce, idan da ina da abin yi zaryar ba zata dameni ba to amma ba bu abin yi don gona ta guda na jinginar in ji shi.
Shi ma Shibi Gamsa, mahaifin daya daga cikin irin wadanann yaran ne, ya shaida wa BBC cewa, 'yarsa aka yi wa tiyata a dubura watanni hudu ke nan, to amma a mayar da duburar ya gagara.
Ya ce, "Ina roko da a taimaka mana a mayarwa da yaranmu duburar da aka fito da musu da ita bayan tiyata tun da ciki ya warke."
Hamisu Bako, shi ne garkuwan sarkin katsinar Maradi ya shaida wa BBC cewa ya bibiyi wannan lamarin don gano abin da ke faruwa a asibitin.
Ya ce,"Muna zaune sai muga mutane na yawo suna cewa a taimakesu suna asibiti ga guzurinsu ya kare, to rannan dai na tambayi wasu daga cikin irin wadanann mutane na ce musu wai me ke faruwa ne? sai suka ce yaransu aka ce za a yiwa tiyata a asibitin amma yinta ya gagara."
To da na ga abin ya yi yawa har mutanen na cewa za su yi zanga-zanga, sai na je asibitin a nan na ji mece ce matsalar, wai rashin likitan da zai yi allurar barci a lokacin tiyata ne ke haifar da dadewa ba yi wa mutane tiyata ba a asibitin, in ji Garkuwar Rarkin Maradin.
Ya ce, a duk asibitin mace daya ce mai yin wannan allurar a duk Maradi.
"To mutane na nan cikin wahala a asibitin na Maradi saboda jiran a yi wa wani nasu tiyata a asibitin."
Duk kokarin da BBC ta yi don ji daga bangaren jami'an lafiya a Maradin ya ci tura.