Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bazoum Mohammad na fuskantar sabbin ƙalubale daga ƴan adawa
A Jamhuriyar Nijar, har yanzu 'yan adawa na ci gaba da ƙalubalantar hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta yanke in da ta wanke ɗan takarar shugabancin ƙasar a jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya Bazoum Mohammed.
Tsohon shugaban mulkin sojan ƙasar, Janar Salou Djibo, ya bayyana shigar da sabuwar ƙara kan batun zama ɗan ƙasa na Bazoum Mohamed.
Yana dai ci gaba da ƙalubalantar ɗan takarar shugabancin jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya ne kan sahihancin kasancewarsa cikakken ɗan Jamhuriyar Nijar, duk da yake, kotun ƙolin ta yanke hukunci game da batun a baya.
A farkon watan Disambar 2020 ne, kotun ƙolin ƙasar ta wanke Bazoum daga zargin cewa shi ba ɗan ƙasa bane.
An dai kwashe tsawon lokaci ana ta cacar-baka tsakanin masu son ganin an soke takarar Bazoum Mohammed bisa zargin da suke cewa shi ba ɗan ƙasa bane da kuma masu kare shi.
Masu fashin baƙi a ƙasar irinsu Abdourahaman Alkassoum, dai na ganin, sabuwar ƙarar, wani salo ne kawai na son nuna bajinta don samun goyon bayan sauran jam'iyyun adawa musamman ma dai MODEN FA Lumana da ke neman wanda za ta mara wa baya a zaben 27 ga watan Disamabar 2020.
Abdourahaman Alkassoum, ya ce ba wani abu bane ya sa wannan batu na Bazoum wai ba ɗan kasa bane yaƙi ci yaƙi cinyewa ne saboda wasu dalilai.
Ya ce,"Dalili na farko shi ne farin jinin da Bazoum ke dashi, da kuma yadda ya samu karɓuwa a wajen 'yan ƙasar".
Mai fashin baƙin ya ce, su kansu jagororin siyasar ƙasar su kansu na da tasu matsalar don haka zasu yi rinƙa yin abubuwa wajen tababtar da cewa sun ɓata Bazoum a idon jama'a.
Karin bayani
Duk waɗannan rigingimu dai na zuwa ne a yayin da babban zaɓen ƙasar ke ƙaratowa abin da ya rage bai wuce ƙasa da makonni biyu ba.
Tun kafin yanke wannan hukunci dai an yi yaɗa jita-jitar cewa kotu ta kori takarar Bazoum Mohammed.