Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Ruwa ta Duniya: Wahalhalun da wasu 'yan Afirka ke sha kafin samun ruwan sha
Matsalar rashin ruwa mai tsafta na ƙaruwa a Afirka kuma mutane na shan wahala sakamakon rashin ruwan sha.
Yayin da yawan mutanen Afirka keƙaruwa da kuma sake rincaɓewar matsalolin sauyin yanayi da ake ganin tasirinsa a kullu-yaumin, ana kiyasta cewa zuwa shekara ta 2025 kusan mutum miliyan 230 za su fuskanci ƙarancin ruwan sha a nahiyar, kuma mutum miliyan 460 za su kasance suna rayuwa a yankunan da ake fuskantar ƙarancin ruwan sha.
Wasu alkaluma da UNICEF ta fitar na cewa mutum 1 cikin 3 a Afirka na fuskantar matsalar ƙarancin ruwan sha.
Yanzu haka akwai mutum miliyan 400 a yankunan kudu da hamadar sahara da kwata-kwata ba sa samun ruwan sha. Mutane irin waɗannan a yankunan na tafiyar aƙalla minti 30 kullum kafin su samu ruwan sha.
Albarkacin bikin ranar ruwa ta duniya da ke duba yadda samun wadatacce da tsaftataccen ruwan sha ke ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga al'umomi da dama a duniya, BBC ta nazarci ƙalubalen da ake ciki a wasu yankunan Afirka.
Najeriya
Kiyasin asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, na cewa sama da kashi 86 cikin 100 na al'ummar Najeriya ba sa samun tsaftataccen ruwan sha.
Ana danganta waɗannan matsaloli na ƙarancin ruwan sha da kuma samun inda za a je domin iya samun ruwa cikin sauƙi.
Duk da cewa akwai rahotanni da ke cewa kusan kashi 76 cikin 100 na 'yan Najeriya na iya samun ruwan sha, sama da rabin wannan ruwa gurbatacce ne.
A cewar rahoton, a rana wadatuwar ruwan 'yan Najeriya ba ta zarta lita 9.
UNICEF ya ce sama da mutane biliyan 1.42 a duniya - ciki har da yara miliyan 450 - na rayuwa a yankunan da ake cikin matsanancin ƙarancin ruwan sha. Wannan na nufin kashi 1 cikin 5 na yara a duniya ba sa samun isasshen ruwa na amfanin yau da kullum.
Alkaluman a Najeriya akwai damuwa, domin akwai yara miliyan 26.5 da ke rayuwa a yankunan da ake matsananciyar wahalar ruwa - kashi 29 kenan na yawan yara a Najeriya. Kusan ana iya cewa kashi ɗaya ciki uku na yara a Najeriyar ba sa samun ruwa a kullum, a cewar UNICEF.
Asusun ya ce tasirin rashin ruwa abu ne da kowa ke ji a jikinsa, amma babu wanda ya fi shiga jigata kamar ƙananan yara.
Wakilin Unicef a Najeriya, Peter Hawkins ya ce ana ganin yada rijiyoyi ke bushewa, yara suke wahalar jigilar ruwa yanayin da ke hana su zuwa makaranta.
Peter ya ce a ko da yaushe idan aka shiga cikin matsala na ruwa ko fari da ambaliyar ruwa, yara ke shiga cikin ukuba da kamuwa da cututtuka.
Jami'in ya ce a halin da ake ciki yanzu da wuya Najeriya ta kai labari wajen cimma muradun ci gaba na SDG, muddin ba a dukufa da daukar matakai masu karfi ba daga ɓangaren masu ruwa da tsaki.
Nijar
Kashi 64 cikin 100 na al'ummar Nijar na fuskantar karancin ruwan sha. Kusan mutum 9 cikin 10 ba su da dabarun zubar da shararsu.
Ruwan da suke sha na tasiri wajen yaɗuwar cututtuka, tsayar da neman ilimi da tasiri a haɓɓakar tattalin arziki, wannan yanayi na taka rawa wajen mutuwar jarirai da ƙananan yara musamman a ƙauyukan Nijar.
Cututtuka masu alaƙa da shan gurbataccen ruwa da tsafta na ɗaya daga cikin masu sanadi mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar.
Samun damar ruwan sha da tsafta abu ne da har yanzu ake karacinsa a Nijar inda ake iya ganin bambanci sosai tsakanin mazauna birni da karkara.
Kashi 56 cikin 100 na al'ummar kasar kawai ke samun ruwan sha. Kuma kashi 13 cikin 100 ke samun damar iya tsaftacce muhallinsu.
Mutane na ba-haya a kan tituna kuma dabi'a ce da kusan kashi 71 cikin 100 na 'yan kasar ke yi wadda ake ganin tasirinta a fannin lafiya da abinci da ilimi da haɓakar tattalin arziki.
Kashi 22.7 cikin 100 na makarantu ke samun ruwan sha sannan kashi 26.7 cikin 100 ke iya aiwatar da tsafta. Akwai ɗalibai mata da dama 'yan makaranta da ba sa iya samun damar tsaftace jikinsu yadda ya kamata da samun wadatuwar auduga.
UNICEF ya ce yana taimaka wa gwamnatin Nijar da hadin-giwar masu ruwa-da-tsakiya wajen bijiro da hanyoyin kawo sauki da inganta samar da ruwan sha da assasa tsafta.
Ghana
Yayin da wasu ƙasashe Afirka ke fama da rashin ruwa, Ghana ita kuwa na fama da matsalar yawan gurbataccen ruwa ne. Ana danganta matsalar da rashin na'urori ko hanyar tace ruwan.
Gwamnatin kasar ta sha shaida cewa za ta duba hanyoyin maye gurbi ko sauya injinin tsaftace ruwan, amma tsadarsu ta kai dala miliyan 35, watakila wannan ba mamaki na sake haifar da tsaiko.
Sauya sheƙa ko balaguron mutanen daga karkara zuwa birni a Ghana na tasiri wajen matsalar sake gurbacewar ruwan sha. Akwai tsarin gidaje da lalacewar hanyoyin ruwansu da ba-haya ke tasiri wajen gurbata ruwan sha.
Wannan na taka rawa ko tilasta wa iyalai neman ruwan sayarwa, wanda akasari ba shi da tsafta. Lamarin da ke ta'azzara amfani da ruwa mara kyau da ke haddasa cututtuka.
Ɗaya daga cikin cuttukan da ake yawaita samu a Ghana saboda wannan matsalar ita ce kwalara. Cutar na yaɗuwa saboda lalacewar magudanan ruwa a gidajen mutane da wajen ba-haya.
Wannan matsalar a 2014 da ta hadu da ambaliyar ruwa ta yi sanadin rasa rayukan mutum dubu 30.
Kashi 73 cikin 100 na al'ummar Ghana ko mutum miliyan 23 na amfani da ruwan da ba su da tsafta. Wannan na nufin 'yan Ghana miliya 3.9 kaɗai ke samun ruwa mai tsafta.
Mahukunta na cewa akwai bukatar gwamnatin Ghana ta tashi tsaye wajen kawar da waɗannan matsaloli da ke ci wa 'yan ƙasar da dama tuwo a ƙwarya.
Akwai kuma sauran ƙasashe irin su Kamaru da kashi 58 cikin 100 na al'ummar ke fuskantar matsananciyar wahala wajen samun ruwan sha, a Chadi al'ummarta kashi 57.5 cikin 100 ba sa samun ruwan amfanin yau da kullum. Haka abin yake a Mozambique tsakanin al'ummarta kashi 52.7 cikin 100.
Ita ma ƙasar Eritrea ta shiga sahun ƙasashen Afirka 10 da ke cikin ukubar rashin ruwa, inda 'yan kasar kashi 80.7 cikin 100 ke fuskantar ƙalubale a fannin samun ruwan sha wadatacce.
Haka kuma lamarin yake a Papua New Guinea da Uganda da Ethiopia da Somaliya da Angola, sai kuma Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.
Waɗanan matsaloli da ake ganin a ƙasashen Afirka da muradan Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyi ake ganin akwai bukatar sake ƙara kaimi da zuba kudade wajen inganta ruwan sha.
Bankin raya ƙasashen nahiyar Afirka ya yi lissafin cewa Afirka za ta bukaci akalla dala biliyan 66 domin wadatuwar ruwa mai tsafta. Wannan bai kunshi dala biliyan 170 ba na samar da dauwamammiyar hanyar ci gaba da samun ruwan a kowanne lokaci cikin sauki.