Matar da aka ɗaure shekara 30 a gidan yari saboda ta yi ɓari

Karen

Asalin hoton, Courtesy of Jennifer Lacayo

Bayanan hoto, An yanke wa Karen hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari a El Salvador a 20215 bayan an zarge ta da zubar da ciki
    • Marubuci, Daga Valeria Perasso and Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Lokacin da Karen ta farka daga barci a wani asibitin El Salvador, ta lura cewa an saka mata ankwa a hannu sannan kuma ga 'yan sanda a gefenta.

"Akwai mutane da yawa a wurin kuma suna ta cewa wai na kashe jaririna kuma 'sai na fuskanci hukuncin abin da na aikata'," kamar yadda Karen ta shaida wa BBC.

Tana buƙatar kulawar gaggawa saboda wahalar zubewar ciki. Amma Karen, mai shekara 22 a lokacin, ta tsinci kanta cikin zargin zubar da ciki.

"Na yi yunƙurin yin bayanin abin da ya faru, amma suka ƙi sauraro na," a cewarta.

"An riga an yi min shari'a har ma an yanke min hukunci a can."

Tsattsaurar doka

El Salvador, da ke nahiyar Tsakiyar Amurka, na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke suka fi tsaurin doka kan zubar da ciki, wadda ta haramta duk wani nau'i na zubar da shi, ko da kuwa na barazana ga rayuwar mace ko an yi shi ta hanyar fyaɗe ko kuma 'yan uwa ne suka yi shi.

Karen, wadda aka tuhuma da kisan kai, an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 30 a gida yari. Tana cikin rukunin mutanen da aka kira "Las 17", waɗanda aka taɓa yanke wa hukuncin ɗauri saboda yin ɓari ko kuma haihuwar jariri babu rai.

Karen ta shafe shekara shida a garƙame kafin daga baya a sako ta tare da wasu mata uku a watan Disamban 2021 sakamakon wani matsin lamba daga ƙasashen duniya.

A lokacin da aka tsare ta, Karen na da ɗa mai shekara biyu.

Karen ba ta sake ganin sa ba har sai da ya kai shekara tara.

Karen (second from right) poses for pictures during a press conference following her release

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An saki Karen da wasu mata uku daga gidan yari a Disamban 2021 bayan masu fafutika sun daɗe suna yekuwa

'Na so na rungume marigayin ɗana a hannayena'

Ɗaya daga cikinsu ita ce Cinthya, wadda aka ɗaure a 2009 kan kisan kai bayan ɗanta ya mutu saboda an haife shi bakwaini. An sake ta a 2019.

Cinthya ta fada wa BBC cewa maimakon a nema mata motar ɗaukar marasa lafiya, 'yan sanda ne suka isa wurin. Ta sume, kuma ko da ta farka a asibiti, kamar Karen, sai kawai ta ga ankwa a hannunta.

An tafi da ita daga asibiti zuwa ofishin 'yan sanda kai-tsaye kafin a fara yi mata shari'a. Ba a ba ta damar gani ko yin magana da 'yan uwanta ba, hasali ma ko gawar ɗan nata ba ta gani ba. Shekararta 20 a lokacin.

"NA so na rungumi ɗana a hannuna, amma ba a ba ni dama ba. Haka ma ba su bar ni na je jana'izarsa ba," in ji Cbthya.

Picture of Cinthya on the beach

Asalin hoton, Courtesy of Cinthya

Bayanan hoto, Cinthya ta shafe shekara 10 a gidan yari karkashin dokar hana zubar da ciki, kuma wasu fursunoni sun kai mata hare-hare saboda laifin da aka ce ta aikata

Karen ta ce ta fuskanci irin wannan matsalar a kotu amma ta yi a cikin bursin saboda ta samu kanta cikin sauran matan da aka ɗaure su bisa tuhumar zubar da ciki.

"Mu kusan 10 ne kuma wasu daga cikin matan sun fuskanci cin zarafi daga wasu fursunonin," a cewarta.

"Daga baya sai muka kafa wata ƙungiya don taimaka wa junanmu."

Tasiri maras daɗi

Ba abu ne mai yiwuwa ba a iya cewa dukkanin cikin da suka zube ba matan ne suka zubar da su ba, amma masu fafutika na cewa dokokin na yanzu na ɗaure matan da ba su zubar da cikin da gangan ba.

Masu kare haƙƙin mata a El Salvador na cewa lamarin ya fi shafar matan da ba su da arziki sosai da za su iya samun kulawa daga asibitoci masu zaman kansu.

Mata kamar Cinthya da Karen.

"Mata matalauta ne suka fuskantar matsala da irin waɗannan dokoki da ke jawo musu tsana kuma suke sa wasu su aikata zubar da cikin," in ji Morena Herrera, wata shahararriyar mai fafutika a El Salvador.

Morena Herrera

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, "Mata matalauta ne suka fuskantar matsala da irin waɗannan dokoki da ke jawo musu tsana," in ji Morena Harrera

Cinthya ta yi iƙirarin cewa lokacin da ake yi mata shari'a ba a bari ta yi magana ba a kotu. Haka nan, ba a bari an kai mata ziyara ba ko kuma yi mata bayani daga lauyan da gwamnati ta ba ta lokacin da take jiran shari'a a gidan yari.

Ba ta ma san tuhumar da ake yi mata ba takamaimai.

"Har sai a kotu sannan na ji cewa ana tuhuma ta da kisan kai," a cewarta.

BBC ta nemi mahukuntan EL Salvador su mayar da martani game da zarge-zargen amma ba mu samu amsa ba.

A cewar alƙaluman wata cibiya da ke Amurka mai suna Center for Reproduction Rights, El Salvador na cikin ƙasashe bakawai a Tsakiyar Amurka da suka haramta zubar da ciki kwatakwata.

Honduras, da Jamaica, da Nicaragua, da Haiti, da Dominican Republican, da kuma Surinam ne sauran ƙasashen (a faɗin duniya kuma, ƙasashen da suka haramta zubar da ciki kwatakwata 24 ne).

'Wani ƙulli ne da ba shi da alamar warwarewa'

Har yanzu akan ɗaure matan da suka yi ɓari a El Salvador. A watan da ya gabata ma an ɗaure wata mace da aka bayyana da "Esme" shekara 30 a gidan yari.

"Har yanzu ana ɗaure mata irina a gidan yari. Wani ƙulli ne da ba shi da alamar warwarewa," a cewar Cinthya.

Bayan an sako ta, Cinthya ta sha wahala wajen neman aikin yi saboda tarihin laifinta, amma sakamakon wani taimako da ta samu daga wata ƙungiya ta samu damar gudanar da harkokin sayar da tufafi.

Cinthya poses with her daughter at her birthday party

Asalin hoton, Courtesy of Cinthya

Bayanan hoto, Tun baya sakinta, Cinthya ta haifi wata yarinya

Ta haifi wata yarinya a 2020 mai suna Marcela Elizabeth.

"Na firgita lokacin da na samu ciki, saboda tsoron zan sake fadawa cikin abin nan idan aka samu matsala," a cewar Cinthya.

"Amma an haife ta ƙalau ba tare da wata matsala ba. Ita ce farin cikina."

Karen ta ce tana jin cewa mutane na nuna mata yatsa amma yanzu ta mayar da hankali kan karatun sakandare da ta fara a gidan yari da kuma sake ƙulla alaƙa da ɗanta.

Karen na ganin bayar da labarinta zai taimaka wa wasu matan.

"Har yanzu akwai abubuwan da ke damu na da ba zan manta da su ba. Amma magana a kansu za su iya taimakawa wajen daƙile faruwar wasu abubuwan kuma ya taimaka wa wasu ƙawayena da har yanzu suke a ɗaure."