Ukraine ta ce ba za ta yarda da sulhun da za ta ba Rasha yankinta ba

Asalin hoton, Getty Images
Mai ba wa shugaban Ukraine shawara, Mykhailo Podolyak, ya ce Kyiv ba za ta bi kiraye-kirayen da ake yi na kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta, da ta kunshi barin dakarun Rasha su ci gaba da zama a yankunan kudu da kuma gabashin kasar ba.
Mista Podolyak ya ce ya kamata shugabannin Turai da Amurka su fahimci cewa alummar Ukraine ba za su taba yarda da saryar da wani yanki na su ba, su sallama shi ga Rasha ba, wadda ya ce ta aikata laifukan yaki a kasar tasu.
Ya ce duk wata yarjejeniya da za a yi yanzu ta dakatar da bude wuta, za ta ba wa Rasha damar sake shiri ne ta farfado, ta sake kaddamar da wani yakin wanda ya fi na yanzu muni nan da 'yan shekaru.
Tun da farko Shugaba Zelensky na Ukraine din ya ce mamayar da Rasha ta yi wa Crimea da Donbas, ta dan wani lokaci ce kawai, a karshe Ukraine ce za ta yi galaba, amma kuma dai ya ce a karshe yakin zai kare ne da yarjejeniya.
Su kuwa a halin da ake ciki mayakan Rasha sun tsananta ruwan wutar da suke yi domin kama Karin yankuna a gabashin Donbas, inda suke ta ruwan bama-bamai a kan inda mayakan Ukraine suke.
Can a yankin arewa maso yammacin Ukraine din Rashar ta ce ta yi nasarar lalata tarin wasu makamai, wadanda kasashen Yamma; na Turai da Amurka suka aika wa Ukraine din.

Asalin hoton, Other
Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na Moscow.
Igor Konashenkov shi ne kakakin sojin Rasha:
Ya ce, ''Sojojin Tarayyar Rasha sun ci gaba da aikin musaman da suke yi a Ukraine. Manyan makamai masu linzami na yankan-shakku, da ke cin dogon zango, wadanda kuma ake harba su daga jiragen ruwa, a kusa da tashar jirgin kasa ta Malin a yankin Zhytomir, sun lalata tarin makamai da sauran kayan yaki wadanda Amurka da kasashen Turai suka aika wa dakarun Ukraine da ke sake haduwa a Donbas.''
Wakiliyar BBC ta ce dakarun na Rasha sun matsa gaba daga inda suke, kuma dangar da Ukraine ta yi ta fara sukurkucewa.
Nasarar da Moscow ta samu ta kama birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwa, wanda ke da muhimmancin gaske, bayan da mayakan Ukraine da aka rutsa a wata ma'aikatar sarrafa karfe tsawon makonni, suka mika wuya, ta karfafa wa Rashawan guiwa.









