Gwarzon mai ɗaukar hoton taurari na 2021: Jerin sunayen da aka fitar
An ƙaddamar da gasar hotunan taurari da suka yi fice a bana ta cibiyar nazarin ilimin taurari ta Royal Observatory Greenwich karo na 13, inda aka bayyana jerin hotuna masu ban mamaki na sararin samaniya da ke takarar lashe gasar.

Asalin hoton, Peter Feltoti
Masu daukar hoton taurari da aka zaɓo sun ɗauko hotunan abubuwa masu ban mamaki daga samaniya da taurari da sauran duniyar samaniya.

Asalin hoton, Vitaliy Novikov
Mutum sama da 4,500 suka shiga gasar daga ƙasashe 75.
Alƙalan gasar sun haɗa da Editan fasaha na shirin sararin samaniya Steve Marsh, da mai wasan barkwanci kuma matashin masanin taurari Jon Culshaw, da sauran masana ilimin duniyar taurari.
Za a nuna hoton da ya yi nasara a bikin baje-koli babban gidan tarihi na National Maritime Museum da ke London a Birtaniya a ranar 18 ga Satumba.
Ga wasu daga cikin hotunan da ke takarar lashe gasar.

Hoton kan dabbar dolfin Nebula na Yovin Yahathugoda daga Sri Lanka

Asalin hoton, Yovin Yahathugoda
Wannan shi ne ya fi jan hankalin mai ɗaukar hoton taurari kuma ya nuna yadda iska da wani yanayi ya samar da wannan sifa a sararin samaniya.
Tauraruwar da ta yi sanadin samar da wannan yanayin ita ce ta fi haske kusa da tsakiyar abin da aka kira nebula kuma an bayyana ta a matsayin tauraruwar Wolf-Rayet.

Harmony, na Stefan Liebermann daga Jamus

Asalin hoton, Stefan Liebermann
Hoton yana nuna yanayi mai ban sha'awa a filin mai furanni a Valensole, Faransa.
Launin furannin da layin da ke tsakani sun bayar da mamaki, ko da yake, haske ya bayyana da bai kamata ba a yanayin.

Iceland Vortex, na Larryn Rae daga New Zealand

Asalin hoton, Larryn Rae
Wannan hoto ne da ya nuna yanayi na tururi mai launin kore a Iceland kuma ya ƙunshi hotuna 20.
Mai ɗaukar hoton ya ci karo ne da wani yanki wanda ya nuna sararin samaniya daidai da yanayin dare cikin ƙanƙara.
Ya fara ɗaukar hoton yanayin, daga baya kuma ya ɗauki kansa yana kan ƙanƙara

Luna Park, na Ed Hurst daga Australia

Asalin hoton, Ed Hurst
Wannan babbar fuskar ita ce hanyar shiga wurin shaƙatawa na Luna Park da ke birnin Sydney.
Tana kallon inuwar gadar Harbour tun 1935, kuma yara a shekaru da dama sun ta yin wasa da tsalle a bakinta tsawon ƙwanaki cikin nishaɗi.
Mai ɗaukar hoton ya ɗauki da dama tare da taurari, ya kuma haɗe su domin nuna yanayi na lokaci.

Fitowar wata akan Bankin Jodrell, na Matt Naylor daga Birtaniya

Asalin hoton, Matt Naylor
Ya kasance babban burin da mai ɗaukar hoton yake son ya cimma na ɗaukar hoton wata da kuma na'urar hangen nesa ta Lovell Telescope.
Ya ɗauko hoton a wurin da ya dace kuma nesa, kuma wata yana sama a lokacin da ya dace.
Yanayin yadda rana ta haska ya bayar da yanani da launi mai kyau.

NGC 2024 - wutar Nebula, na Steven Mohr daga Australia

Asalin hoton, Steven Mohr
Wutar Nebula, da ake kira NGC 2024 da Sh2-277, wata fashewa ce ta nebula kusan shekaru 900 zuwa 1,500 nesa da duniya.

NGC 3981, na Bernard Miller daga Amurka

Asalin hoton, Bernard Miller
NGC 3981 tauraro ne da ya warwatsu kusan shekarun haskensa miliyan 65.
Yanayin hasken ya bazu zuwa rassa da kuma haduwa da wasu taurarin.

Wani ɓangare na wata da ya haskaka birni, na Remi Leblanc-Messager daga Faransa

Asalin hoton, Remi Leblanc-Messager
Wanda ya ɗauki wannan hoton ya yi fatan ɗauko cikakken wata, a tsakiyar hoton, domin raba duniya da samaniya.
Matar da ke tsaye a saman gida za ta zama tsakanin Paris da samaniya.

Taurarin Pleiades ƴan uwan juna, na Jashanpreet Singh Dingra daga Indiya

Asalin hoton, Jashanpreet Singh Dingra
Wannan fitaccen hoto ne na taurari masu haskakawa a yankin mai ɗaukar hoton a lokacin sanyi.
Pleiades, wanda ake kira taurari bakwai ƴan uwan juna da Messier 45, taurari ne a bayyane da kuma matsakaicin samfurin tauraron hot B a yankin arewa maso yammacin Taurus.

Duniyar Saturn na Damian Peach daga Birtaniya

Asalin hoton, Damian Peach
A cikin wannan hoton, duniyar Saturn ta nuna wadatattun bayanai a sassan duniya.

Taurari sun ratsa birnin Lujiazui City Skyline, na Daning Kai daga China

Asalin hoton, Daning Kai
Wannan hoton ya nuna ratsin taurari a samaniyar birnin Lujiazui city a gundumar Pudong na China.
Mai daukar hoton ya ɗauki wannan hoton a hasken dare.

Mai kallon taurari, na Yang Sutie a China

Asalin hoton, Yang Sutie
Yayin da mai ɗaukar hoton yake kan tuƙi a kan hanya mai tsaunuka cikin dare ya juya cikin kwana, sai ya ga wani tsauni a gefen dama na hanyar.
Ya tsaya ya hau sama a gefen hanyar ya fito da kyamararsa ya ɗauki hoton nan take, sannan ya yi gaba da zuwa baya a wannan da'irar
Daga nan ya hau saman tsaunin ya tsara kansa a hoton.

Fitowar rana a Magic City, na Jiajun Hua daga China

Asalin hoton, Jiajun Hua
An ɗauki wannan hoton kilomita 16 daga unguwar hada-hadar kasuwanci ta Lujiazui a Shanghai.
Duk shekara makwanni ne kawai masu ɗaukar hoto ke samun damar ɗaukar irin wannan hoton na fitowar rana a yankin.

Ion Tail of Comet 2020F8 SWAN, na Gerald Rhemann daga Austria

Asalin hoton, Gerald Rhemann
A wannan hoton tauraro yana nuna wani fasali da yanayi na tauraruwa mai wutsiya.
Ƙalubalen da ke tattare da hoton na tauraruwa mai wutsiya ba wai kawai nuna motsin taurarari ba ne, amma kuma ta hanyar la'akari da saurin sauyin sifofin taurarin.

Hoton The Soul of Space na Kush Chandaria daga Birtaniya

Asalin hoton, Kush Chandaria
Soul Nebula na ɗaya daga cikin abubuwa masu ban mamaki da duk yadda ka yi ƙoƙarin auna na'urar hangen nesa, za ku samu wasu abubuwa na ban mamaki da bayanai da za iya ganowa.
Tsawon sa'a 14 da tsarawa, bayanai da sifofi nebula sun fara bayyana.










