Dakarun Rasha sun gamu da cikas a yunkurin shiga Kyiv

Asalin hoton, BBC/LEE DURANT
Wani yanki na garin Bucha ya kasance daya daga cikin wuraren da suka zama tamkar makabarta ga burin Rasha na yin kawanya da shiga babban birnin Ukraine, Kyiv, domin hambarar da gwamnatin Shugaba Volodymyr Zelensky.
Rasha ta tafka asara ne kwana biyu ko uku bayan da dakarunta suka tsallaka zuwa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, inda dakarun Ukraine suka murkushe yunkurin masu mamayar ta hanyar tarwatsa manyan motocin yaki na igwa-igwa na Rasha da sauran motoci dauke da soji, da ke tafiya ta cikin garin na Bucha kan hanyarsu ta zuwa Kyiv.
Dakarun Ukraine sun yi nasarar tarwatsa tawagar ta sojin Rasha, a wannan hari da ya kasance daya daga cikin na farko na da yawa na kwanton-bauna, da ya taka wa mamayen na Rasha birki.
Tawagar BBC ta samu damar kaiwa ga garin na Bucha saboda janyewar da Rasha ta yi, a abin da fadar gwamnatin Rasahr, Kremlin ta bayyana wani mataki na kokarin mayar da hankali a kan yakin a gabashin Ukraine.
Moscow ta ce ba tare da wata cikakkiyar sheda ba cewa ta cimma burinta a yakin da take yi a tsakiyar Ukraine, kuma wai daman ba ta da niyyar lalle sai ta kama babban birnin kasar Kyiv.
Sai dai ana ganin gaskiyar lamarin ita ce, Rashawan sun gamu da tirjiye da cikakken tsari na dakarun Ukraine da ba su yi tsammani ba, a yunkurinsu na shiga babban birnin.
Kuma shedar da ta tabbatar da hakan ta hada da tarkacen da za a iya gani na manyan motocin yaki da igwa-igwa na Rasha, da har yanzu suke zube a titunan wajen garin na Bucha.

Asalin hoton, BBC/KATHY LONG
Masu aiko da rahotanni sun ce, wurin da aka yi wa Rashawan wannan kwanton-bauna, titi ne ziri, kuma mikakke, wanda daman za a iya yin nasara hakan.
Wadanda suka ga barnar, sun ce dakarun Ukraine sun yi amfani da kananan jiragen sama na yaki ne marassa matuka da aka kawo daga Turkiyya.
Wasu mazauna kusa da wurin sun ce masu sa-kai da ke taimaka wa sojin Ukraine ma sun kasance a yankin a wannan lokaci na harin.
Inda sojin suka ritsa tawagar dakarun Rasha da ke gaba, sannan kuma wasu suka datse bayan, aka yi musu rubdugun da ya haddasa musu wannan mummunar barna, da ta sanya su fasa kutsawa ta garin na Buchan a yunkurin kama Kyiv.
Har yanzu ana iya ganin tarin barnar da aka yi wa Rashar, a wannan ziri, inda tarkacen kayan yakin sojin nata da suka kone ke warwatse.
Rahotanni sun ce matasan da Rasha ta sanya a aikin soji 'yan shekara 18 zuwa 20 wadanda wannan hari ya rutsa da su, wasu sun tsere inda suke rokon mutanen yankin da kada su mika su ga sojin Ukraine.
Sai dai kuma wasu rahotannin sun nuna cewa sojin Rashar da suka ja da baya daga garin na Bucha, ba su nuna tausayi ba.
Domin sojojin Ukraine da suka shiga birnin daga baya sun ga gawarwaki akalla 20 zube a titi, na mutanen da Rashawan suka hallaka.
Wasu daga cikinsu an daure hannuwansu a baya. Magajin garin ya ce sun binne gawarwaki 280 a manyan kaburbura.









