Hotunan majami'u da wuraren tarihi na addini a Ukraine da aka ɗaiɗaita saboda yaki

The priest of Yasnohorodka, stands inside his church destroyed because the combats between the Russian and Ukrainian armies

Asalin hoton, NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, Malamin cocin da ke Yasnohorodka, kusa da Kyiv, yana tsaye a cikin cocinsa da aka lalata
    • Marubuci, Daga Jack Hunter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
1px transparent line

Ukraine ta zargi Rasha da laifin rusa ko lalata wuraren ibada akalla 59 da ke fadin kasar tun lokacin da ta kaddamar da yaki a kasar.

Cikin wadanda aka lalata har da babbar majami'a ta masu ra'ayin mazan-jia da aka daidaita, da makarantar Yahudawa da aka yi wa luguden-wuta, da majami'u na gama-gari.

Kai hari kan gine-ginen tarihi da kuma wuraren tarihi na al'adun gargajiya aikita laifukan yaki ne a tsarin kasashen duniya, a cewar yarjejeniyar da aka kulla a birnin Hague.

Rasha ta musanta kai hari a wuraren da fararen-hula suke zaune, amma BBC ta gano wuraren ibada da dama da aka lalata ko rusawa baki daya.

Babbar majami'a da aka yi wa luguden-wuta

Ofishin yawon bude-ido na Mariupol ya bayyana babbar majami'ar St Michael' Cathedral a matsayin "wuri mafi kyawu" a yankin Left Bank da ke birnin.

Daga babban majami'ar, wadda aka bude a 1997, ana iya ganin " Kogin ​​Azov, da tsaunuka koraye da kauyuka da ke bakin teku" - kuma masu ayyukan ibada da masu kai ziyara suna son zuwa wurin, a cewar ofishin.

St Michael's Cathedral stock photo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kafin yakin da Rasha ta kaddamar, ana iya ganin yankunan gefen teku da ke Mariupol daga babbar St Michael's Cathedral
1px transparent line

Sai dai hasumiya da wasu bangarori na babbar majami'ar ta masu ra'ayin mazan-jiya sun lalace sakamakon luguden-wutar da dakarun Rasha suka yi a birnin mai tashoshin jiragen ruwa da ke kudancin kasar.

St Michael's Cathedral

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babbar majami'ar St Michael's Cathedral da ke Mariupol ta lalace sakamakon luguden-wuta
1px transparent line

An lalata tagogin gilasai na babbar majami'ar, kuma an yi wani wawakeken rami a jikin bangwayenta masu launin ja.

St Michael's Cathedral

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An rusa tagogin cocin, sannan an cire kubbarta, kuma an lalata kankaren da ke jikinta
1px transparent line

Cocin gama-gari da aka ɗaiɗaita

An kai hari kan wata coci da ke karamin kauyen Yasnohorodka, wanda ke da nisan kilomita 40 daga yammacin Kyiv, a cewar Cocin Masu ra'ayin mazan-jiya ta Ukraine.

Roman, priest of Yasnohorodka, stands in front of his church

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malamin coci Romanov da ke Yasnohorodka yana tsaye a kusa da ginin cocin bayan an yi mata luguden-wuta
1px transparent line

Ta ce an yi ruwan wuta a kan kubbar cocin Church of the Nativity of the Blessed Virgin ranar 5 ga watan Marisa, inda aka lalata wasu bangarori nata.

Kazalika an yi ruwan harsasai da babbar bindiga a tagogi da kofofin cocin.

A yayin da ake tsaka da yaki, dakarun Rasha sun kai hari a kauyen da ya yi sanadin wani malamin coci a wata majami'ar.

Priest Romanov is seen inside a damaged church following recent shellings in Yasnohorodka,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Baraguzan gini sun cika cocin bayan an yi luguden-wuta sau biyu a kanta
1px transparent line

An kai hari kan wurin bautar Yahudawa

Wani luguden-wuta da Rasha ta yi ya yi wani rami a rufin yeshiva, wurin da a baya ya kasance dakin karatu, a Kharkiv, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a Ukraine, a cewar al'ummar Yahudawan birnin a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ana amfani da ginin na yeshiva a matsayin wurin bautar Yahudawa da makarantar sakandare da kuma wurin kwanan dalibai, a cewar al'ummar ta Yahudawa.

Damage from shelling on yeshiva

Asalin hoton, JewishKharkov/Facebook

Bayanan hoto, Harin da aka kai da roka ya cire rufin ginin wurin bautar Yahudawa na yeshiva a Kharkiv
1px transparent line

"Rokar da aka harbo ba ta fashe ba amma ta yi wagegen rami a rufin ginin," a cewar matar babban limamin Yahudawan Kharkiv, Moshe Moskovitz, a hirarta da shafin intanet na Yahudawa mai suna 0404.

Harin ya sa shugaban Wuraren Bautar Yahudawa na duniya, David Ben-Na'eh, ya aike da wasika zuwa ga shugabansu na Rasha, Berel Lazar, inda ya nemi ya roki Shugaba Vladimir Putin ya dakatar da dakarunsa daga rusa wuraren ibada.

Rasha ta musanta kai hari garin Yahudawa

A jawabin da ya yi wa majalisar dokokin Isra'ila a makon jiya, shugaban Ukraine Zelensky ya yi ikirarin cewa dakarun Rasha sun kai hari a garin Uman, wurin da Yahudawa mabiya Hasidic suke karramawa.

Mr Zelensky, wanda shi ma Bayahude ne, ya ce rokokin da Rasha ta harba sun lalata gari a ranar farko da ta soma kai hare-hare a watan Fabrairu. Dubban Yahudawa mabiya Hasidic ne suke zuwa Uman duk shekara domin bikin ranar Rosh Hashanah inda suke kai ziyara a kabarin limamin Yahudawa Nachman na Breslov, wanda ya jaddada darikar Hasidic sanna ya mutu a 1810.

Religious Jews perform tashlikh, a Jewish atonement ritual, at a lake formed by the Umanka River on the first day of Rosh Hashanah on September 10, 2018 in Uman, Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban Yahudawa mabiya Hasidic ne suke zuwa Uman duk shekara domin bikin ranar Rosh Hashanah inda suke kai ziyara a kabarin limamin Yahudawa Nachman na Breslov

Sai dai Rasha ta musanta ikirarin, inda ta fitar da hotunan abin da ta kira dakarun Ukraine da ke dauke da makamai a kusa da wata coci da ke garin.

line
line

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka