Rikicin Ukraine da Rasha: Martanin da shugabannin duniya ke yi ga Putin

People walk at the border crossing between Poland and Ukraine

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An shirya kan iyakar Poland da Ukraine don tarbgar 'yan gudun hijira
An wallafa

Manyan ƙasashen yammacin duniya sun yi ta mayar da martani kan kutsen da Rasha ta yi cikin Ukraine, suna zarginta da dawo da yaƙi baya a Turai.

Shugaban Amurka Joe Biden na fargabar kar a samu munanan asarar rayuka ya kuma ce ƙawayen Amurka za su ƙaƙaba wa Rasha takunkumai masu tsanani.

A gabashin Turai kuwa, fargabar na ƙaruwa ne saboda tunanin halin da za a shiga na kwararar ƴan gudun hijira.

Sauran ƙasashen sun haɗa da China, wacce ta ƙi yarda da kalmar kutse da ake ambata sannan ta yi gum da bakinta. Wasu kuma sun fi mayar da hankalinsu ne kan ƴan kasarsu da ke zaune a Ukraine.

Ukraine ta ce Rasha na kai hare-hare babau ƙaƙƙautawa daga kowane ɓangare, amma har yanzu babu wasu bayanai kan irin ɓarnar da aka samu.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi magana kan wani aikin soji na musamman kan kawar da sojoji da aƙidar ƴan Nazi ta Hitler daga Ukraine, amma ba a bayyana sauran manyan burikan nasu ba.

Faɗa mana labarinku: Idan ku 'yan Najeriya ne da ke zaune a Ukraine, a wane hali kuke ciki yanzu?

Rashin tabbas ɗin da ake ciki bai hana ƙasashen Turai da suke ƙawance ci gaba da nuna fushinsu ba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce wannan wani lokaci ne da aka samu sauyin al'amura a tarihin Turai.

'Ɗanɗana kuɗa' - Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai

Mafi yawan ƙasashe sun yi magana ne a kan yin tur da kuma alƙawuran saka takunkumai.

Joe Biden ya ce: "Shugaba Putin ya zaɓi ɗaukar matakin yin yaƙi gaba-gaɗi ne wanda zai jawo munanan asarar rayuka da sanya mutane cikin wahala."

Ya ƙara da cewa Amurka za ta gana da ƙawayenta don sanya takunkuman tattalin arziki a matsayin azabtarwa.

Shugabar hukumar Turai Ursula von der Leyen ta ce Mista Putin za a ɗora wa alhakin mayar da Turai cikin halin yaƙi. Takunkuman za su raunana tattalin arzikin Rasha da ƙoƙarinta na zamanantar da abubuwa.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce Mr Putin ya zaɓi bin hanyar zubar da jini da yin ɓarna ta hanyar kai "hare-haren tsokana."

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce yana tare da abokansa a gabashin Turai, yana mai cewa Mista Putin zai ɗanɗana kuɗarsa kan wannan kuskuren da ya tafka.

Da yake kira kan wani taron Nato na gaggawa, Mr Macron ya nuna goyon bayan ƙasarsa ga Ukraine.

Mataki ne da ƙasashe da dama suka ɗauka, da suka haɗa da Firaminsitan Italiya Mario Draghi, wanda ya kira harin na Rasha da rashin adalci wanda ba shi da hurumi.

Amma akwai matuƙar damuwa kan abin da ka iya faruwa nan gaba.

Wani ministan Jamus ya yi magana kan "yaƙi ya ɓarke a Turai abin da a baya muke tsammanin a labaran tarihi kawai ake jin su", yayin da Ministar Harkokin CIkin Gida Nancy Faeser, ta ce Jamus za ta taimaka wa maƙwabtanta idan har aka samu tururuwar ƴn gudun hijira.

'Matsanancin hali' - Gabashin Turai

Makwabtan Ukraine ma na cikin irin wannan damuwar, amma da yawansu sun fi damuwa kan tsaron su.

Shugaban ƙasar Lithuania, wacce mamba ce ta ƙungiyar Nato, ya ce zai sanya dokar ta ɓaci a ƙasarsa.

Ita ma Maldova da ke can daga kudu irin wannan doka take son ɗauka.

Rahoranni sun ce an ga gwamman motoci sun yi cincirindo a layi a kan iyakar Ukraine, inda Maldova ke cewa za ta karɓi dubban ƴan gudun hijira.

Romania ma ta ce za ta karbi baƙuncin mutum 500,000.

Poland na ta tsara wuraren karɓar ƴan gudun hijira. Ta umarci Rasha da ta kawo ƙarshen hare-haren ta kuma bar Ukraine ta sha iska.

Georgia - wacce ta yi faɗa da Rasha a shekarar 2008 kan wasu yankuna masu taƙaddama - na goyon bayan Ukraine, tana mai cewa hare-haren Rasha za su yi illa kan al'ummomin duniya.

Ita kuwa Belarus ƙawar Rasha, cewa ta yi ba za ta shiga faɗan sojin ba, amma za ta duba yiwuwar yin hakan idan aka nemi ta yi. Belarus ta karɓi baƙuncin dakarun Rasha a yayin rikicin, kuma sun tsallaka daga ƙsar zuwa cikin Ukraine a yayin kai hare-haren.

Ukraine ta umarci Turkiyya wadda mamba ce ta Nato da ta kulle mashigin Bosphorus da Dardanelles don hana jiragen ruwan Rasha wucewa.

Turkiyya ta ce za ta duba yiwuwar buƙatar kuma ta goyi bayan samun ƴancin kan da Ukraine ke fafutuka.

'Salon ƙasashen yamma na malkwaɗa zance' - China

Akwai matuƙar buƙatar jin ta bakin China kan irin martanin da za ta mayar. Martanin na farko kira ta yi da a daina amfani da kalmar kutse, tana mai cewa "salo ne da kafafen yaɗa labaran ƙasashen yamma ke amfani da shi",

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce "ba za mu yi riga-malam masallaci ba".

Wani babban jami'in diflomasiyya Wang Yi ya ce China ta fahimci batun tsaron da Rasha ke nuna damuwa a kai.

China da Rasha suna da ƙawance na ƙut da ƙut da nufin daƙile tasirin Amurka, wanda aka ƙulla a lokacin da Shugaba Putin da Shugaba Xi suka gana kafin Gasar Olympics ta hunturu a Beijing.

China ta shaida wa ƴan kasarta da ke Ukraine cewa su yi ta ɗaga tutar China don kare kansu.