Abu biyar da gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya suka cimma a taronsu

Asalin hoton, Gombe state government
Kungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya ta kammala taron da ta gudanar ranar Litinin a birni Damaturu na jihar Yobe inda ta tattuna a kan kalubalen da yankin ke fuskanta domin neman hanyoyin warwaresu.
A wata sanarwar bayan taro da ta fitar, kungiyar ta ce an samu ci gaba sosai a fannin tsaron yankin saboda an samu mayakan Boko Haram da dama da suka mika wuya ga hukumomi.
Sai dai kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta nemi hanyar da za ta bi wajen sake tsungunar da su a cikin al'umma.
Daya daga cikin gwamnonin da suka halarci taron, gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya shaida wa BBC sake tsugunar da tubabbun mayakan na Boko Haram na cikin batutuwan da gwamnonin yankin suka nuna damuwa a kai.
"Mun ga cewa a yanzu nasara ta tabbata saboda 'yan Boko Haram suna saranda amma mun fahimci cewa akwai abubuwa da za su iya tasowa ganin cewa gwamnati ba ta dauki mataki na ganin yadda za a sake shigarsu da su su zauna cikin alumma ba," in ji shi.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa a kan yadda ake samun karuwar rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma masu satar mutane domin neman kudin fansa a yankin.
Game da haka ne kungiyar ta kuduri anniyar daukar matakan dakile matsalar tun kafin ta yi kamari a yankin.
A cewar gwamna Inuwa: "Mun dauki matakan ganin cewa za mu sa duk abin da ya kamata, da karfinmu da dubarunmu da hikimominmu da karfinmu da kuma na jami'an tsaro da gwamnatin tarayya wajen ganin an samu sauki.
A sanarwar da Isa Gusau, mai magana da yawun gwamnan jihar Borno kuma shugaban kungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabas, Babagana Umara Zulum, ya fitar ya kara da cewa gwamnonin sun amince da matakai biyar.
- Gwamnonin sun ce an samu kyautatuwar tsaro musamman ganin yadda mayakan Boko Haram suke mka wuya inda suka yaba wa gwamnatin tarayya. Sai dai sun nemi a samar da wani shiri kan inganta rayuwar tubabbatun mayakan na Boko Haram
- Gwamnonin sun tattauna kan wani jawabi da ministan harkokin wutar lantarki ya yi kan samar da hasken lantarki a yankin. Sannan suka bayyana mamakinsu na kwashe shekara daya babu wutar lantarki a Maiduguri. Kana suka bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakin da ya dace.
- Kazalika gwamnonin sun tattauna sosai kan shirin samar da hasken lantarki daga madatsar ruwa ta the Mambilla. Sun yi kira ga majalisar dokokin tarayya da gwamnatin tarayya su sanya kudin aikin samar da hasken lantarki a kasafin kudin 2022.
- Gwamnonin sun ce ko da yake kasafin kudin 2022 yana gabar karshe wajen amincewa da shi, amma sun yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta ware isassun kudi da za a gudanar da manyan ayyuka a yankin.
- Kungiyar ta amince gwamnonin su gudanar da taronsu na gaba a ranar 9 zuwa 11 ga watan Maris na 2022 a birnin Gombe.
Wannan shi ne karo na shida da gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka da da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da kuma Bauchi suke taro.
Yankin ya shafe shekaru 12 yana fuskantar tsahin hankalin daga mayakan Boko Haram musaman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.












