'Muna nazari kan hukuncin kotu na biyan Sarki Sanusi diyya'

S T YAKASAI

Asalin hoton, S T YAKASAI

An wallafa

Gwamantin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce tana nazari a kan hukuncin da wata babbar kotu da ke birnin Abuja ta yanke na gwamnatin ta biya tsohon Sarki Kano Muhammadu Sanusi na II diyyar naira miliyan 10 tare da neman gafararsa bisa korarsa daga jihar.

Kwamishinan shari'a na Kano Barista Musa Lawan ya shaida wa BBC cewa sai bayan gwamnati ta yi nazari kan hukuncin kotun sannan za ta san mataki na gaba da za ta dauka

"Mun sa lauyoyinmu su nemi kundin shariar domin mu yi nazari mu duba shi don mu san ko za mu daukaka kara ko a'a", in ji shi.

Ya kara da cewa kundin tsarin mulki ya ba su dama su duba su gani ko kotu ta yi hukuncin da ya dace.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce Sarki Mihammadu Sanusi na II ba shi ne sarki na farko da aka kora daga kasar Hausa a tarihi ba.

"Ita dai kasar Hausa kasa ce mai tarihi da yawa, kuma kowa ya san cewa tarihi ya nuna cewa duk wani sarkin da aka cire ko ya sauka da kansa shi ne ya ke fita daga kasar".

Sai dai ta ce akwai sarakuna da dama a baya da aka dauke su aka kai su wani wuri kuma ya kamata duk wani sarki da aka cire ya ba masaurata girmamawar da ta dace.

Amma kuma wasu na ganin cewa ya kamata a ba sarkin da aka cire damar zabar wurin da ya ke son ya koma da zama.

Muhammadu Sanusi na II bai kalubalanci sauke shi daga kan mulki ba, amma ya nemi kotun ta bayar da umarni a sake shi daga tsarewar da aka yi masa a wancan lokacin da kuma dawo masa da 'yancinsa na kasancewarsa dan adam.

Kazalika, ya nemi kotu ta hana wadanda ya kai kara tsangwamar sa da kuma keta hakkinsa na dan adam.

Sai dai kotun ta ce korar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa tsohon Sarkin na Kano daga jihar "haramtacciya ce kuma ta saba wa kundin tsarin mulkin" Najeriya.

Kotun ta umarci kwamishinan shari'a na Kano ya wallafa neman gafarar a jaridu biyu na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya rawaito mai shari'a Anjuli Chikere tana cewa dokar majalisar sarakunan Kano ta 2019 wadda Gwamna Ganduje ya yi amfani da ita wajen korar tsohon sarkin daga jihar, bayan an sauke shi daga kan sarauta ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.