A cikin hotuna: Yadda guguwar Arwen ta jawo zubar ƙanƙara da ƙaƙƙarfar iskar a Ingila

Waves break around lighthouse

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, An shawarci mutane su guji zuwa bakin teku saboda igiyar ruwa na kaɗawa
An wallafa

Guguwar Arwen ta jawo ƙaƙƙarfar iska mai ƙarfin gudun mili 98 a cikin awa ɗaya, da kuma kaɗawar igiyar teku da zubar dusar ƙanƙara a cikin ƙarshen mako.

An bayar da gargaɗi tun daga ƙarfe 3 na yamma agogon GMT a ranar Juma'a har zuwa Asabar da safe tun daga arewa maso gabas har cikin Scotland.

Mutum uku ne suka mutu sakamakon faɗa musu da bishiyoyi suka yi inda kuma wutar lantarkin dubban gidaje ta ɗauke.

Ga dai wasu zaɓaɓɓun hotuna daga faɗin ƙasar na yadda guguwar Arwen ta yi illa.

Fallen tree in North Tyneside

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Wata bishiya ta rabe biyu a New York da ke North Tyneside, har ta lalata wata mota da ke kiusa da ita
Tree on Metro line

Asalin hoton, NEXUS

Bayanan hoto, A ranar Asabar da Lahadi kuwa lamarin ya shafi harkokin sufurin jirgin ƙasa har aka dakatar da aiki
People play in snow around the Angel of the North

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Wasu mutanen kuwa dadin yanayin suka ji
Swans swim by snow in Lichfield

Asalin hoton, BBC Weather Watcher Belle

Bayanan hoto, Abin ya shafi mafi yawan yankunan ƙasar da suka haɗa da Lichfield a Staffordshire
Person walks through heavy snowfall in a village

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Dusar ƙanƙara mai aywa ta yi ta zuba a Yorkshire Dale, kamar yadda wannan hoton ke nunawa
Sheep in snow

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Mazauna yankin Yorkshire sun wayi gari a ranakun Asabar da Lahadi dusar ƙanƙara ta lulluɓe yankunansu
Man and woman walking in snow

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Yanayin bai hana waɗannan mutanen tafiya a yankin Grinton Moor da ke North Yorkshire ba...
Man and woman rambling in snow

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, ... da ma wadannan mutanen su ma a kusa da Buxton
Snow covers cars at Tan Hill

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Ƙanƙara ta lulluɓe motoci da gidaje a yankin Tan Hill Inn a North Yorkshire har tsawon kwana uku
Aerial view of snow covered houses and streets

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Garin Lee Park ma a Liverpool ƙanƙara ce ta lulluɓe su
Cottage covered in snow

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haka ma garin Leek a Staffordshire dusar ƙanƙara ta lulluɓe shi
Snow falls in Coventry

Asalin hoton, BBC Weather Watcher Tambotaylor

Venus de Milo - now nicknamed Venus de Mi-snow - was sculpted by a mystery Sheffield artist in Endcliffe Park on Sunday afternoon

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.