A cikin hotuna: Yadda guguwar Arwen ta jawo zubar ƙanƙara da ƙaƙƙarfar iskar a Ingila

An wallafa

Guguwar Arwen ta jawo ƙaƙƙarfar iska mai ƙarfin gudun mili 98 a cikin awa ɗaya, da kuma kaɗawar igiyar teku da zubar dusar ƙanƙara a cikin ƙarshen mako.

An bayar da gargaɗi tun daga ƙarfe 3 na yamma agogon GMT a ranar Juma'a har zuwa Asabar da safe tun daga arewa maso gabas har cikin Scotland.

Mutum uku ne suka mutu sakamakon faɗa musu da bishiyoyi suka yi inda kuma wutar lantarkin dubban gidaje ta ɗauke.

Ga dai wasu zaɓaɓɓun hotuna daga faɗin ƙasar na yadda guguwar Arwen ta yi illa.

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.