Dalilin da ya sa Kurɗawan Iraƙi ke jefa rayuwarsu cikin hatsari don su je Turai

...

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Akasarin maza 27 da mata da kuma yaran da suka rasu a mashigin ruwan Ingila a ranar Laraba a daidai lokacin da suka yi ƙoƙarin tsallakawa daga Faransa zuwa Birtaniya a cikin wani kwale-kwalen da aka hura wa iska Kurɗawa ne daga Iraƙi.

Hakazalika wasu Kurɗawan Iraƙi sun rasu a ƴan makonnin nan a kan iyakar Belarus da Poland a daidai lokacin da ɗaruruwan mutane suka yi ƙoƙarin shiga Tarayyar Turai cikin yanayi mai sanyi.

Wannan lamarin ya bar mutane da dama suna ta tambaya kan dalilin da ya sa jama'a daga yankin Kurɗawa daga Iraƙi, waɗanda ke da arziƙin man fetur da kuma tsaro daidai gwargwado ke son jefa kansu cikin wannan hatsarin.

Kurɗawa da dama na Iraƙi waɗanda suke zaune a wasu sansanoni a arewacin gaɓar tekun Faransa da kuma kan iyakar Belarus sun ce sun fito ci rani ne domin guje wa wahalhalun rayuwa da kuma samar wa kansu rayuwa mai inganci.

..

Asalin hoton, Getty Images

Suna ta ƙorafi kan yawaitar rashin aikin yi da kuma ƙarancin albashi da rashin biyan su da rashin kulawar gwamnati da cin hanci da rashawa.

"Babu wani tabbaci a Kurdistan. Dole ne kowane matashi ya yi hijira sai dai kawai waɗanda suke samun goyon bayan jam'iyyu masu mulki," kamar yadda wani matashi a wani sansani da ke Dunkirk ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Pishti.

Wata mata a dai sansanin ta bayyana cewa mijinta ya yi aiki da dakarun yankin na tsawon shekaru, amma dole ne suka koma Turai bayan aka ƙi biyanshi na tsawon watanni.

"Muna sa ran kyakkyawar da zarar mun isa can (Birtaniya), da kuma rayuwa mai kyau ga ƴaƴanmu."

Matsin tattalin arziƙi

Yankin Kurdistan na da adadin sama da mutum miliyan biyar, inda kusan mutum miliyan 1.3 na aikin gwamnati.

Wannan na nufin dole ne iyalai su sha wahala bayan da gwamnatin ƙasar ta yanke albashin ma'aikata da kashi 21 cikin 100 a farkon shekarar da ta gabata da kuma ƙin biyan ma'aikatanta albashi na tsawon watanni sakamakon matsin tattalin arziƙin da annobar korona ta jawo da kuma faɗuwar farashin mai a duniya da kuma rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da ke Bagadaza kan batun kasafin kuɗi.

1px transparent line
..
1px transparent line

Duk da cewa an dawo da biyan albashin a watan Yulin nan, babu tabbaci idan ma'aikatan sun samu kuɗin da suke bi.

A yanzu dai farashin man fetur ya soma farfaɗowa haka ma tattalin arziƙin ƙasar, amma kuma akwai ƙarancin ayyukan yi, akwai kuma ƙarancin albashi da kuma talauci wanda yake haddasa zanga-zanga.

A wannan makon, dubban ƴan jami'a ne suka fito kan titunan manyan biranen ƙasar, wato Irbil da Sulaimaniya inda suke neman a koma biyan tallafin da aka dakatar da bayarwa tun a 2014 bayan faɗuwar farashin mai da kuma soma yaƙin masu iƙirarin jihadi na IS.

"Akwai wasu ɗalibai da ba za su iya biyan kuɗin da za su koma lardunan su ba, da kuma wasu da ba su da kuɗin da za su ci abinci sau uku a rana," kamar yadda wani ɗalibi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wasu daga cikin zanga-zangar da aka gudanar sun koma tarzoma, inda mutane suka rinƙa cinna wa gine-gine wuta da kuma ofisoshin gwamnati da na jam'iyyu. Hukumomin tsaro sun kama gwamman mutane.

Sai dai gwamnatin ƙasar na shan caccaka kan ƙoƙarin da take yi na daƙile lamarin. A watan Mayu, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi ga ƴan jarida da masu kare haƙƙin bil adama da masu zanga-zanga waɗanda suka caccaki hukumomi sun jefa rayuwarsu cikin hatsari ba wai na cin mutuncinsu ko kuma kama su ba, amma har da iya kama su da laifin ɓata suna da kuma lamuran da suka shafi tsaron ƙasa.

Faɗa da Turkiyya

Ƙaruwar rikici a kusa da iyakar Turkiyya daga arewa na daga cikin abubuwan da ake ganin suka haddasa Kurɗawa barin yankunansu inda ɗaruruwan mutane daga garuruwan Duhok da ke lardin Shiladze da kuma garin Deralok - na daga cikin wuraren da aka bayar da rahoton cewa mutanen garuruwan na son zuwa Turai ta Belarus da bazara.

Ƙungiyoyin ƴan tawaye na Ƙurɗawa wato PKK na amfani da tsaunukan da suka zagaye fagagen dagan Turkiyya da Iraƙi a matsayin sansanoni inda suke ta fafutuka da yaƙin kafa ƙasar Ƙurɗawa daga Turƙiyya tun a 1984 kuma tuni Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai duk suka ayyana ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda.

.

Asalin hoton, Getty Images

An bayyana cewa rundunar sojin Turkiyya ta ƙara yawan hare-haren da take kai wa ƙungiyar ƴan tawaye ta PKK tun a watan Afrilu, inda suka rinƙa amfani da jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa inda suka rinƙa yin ruwan wuta ga manyan yan tawayen PKK haka kuma sojojin Turkiyya sun ta yaƙar PKK a ƙasa a arewacin Iraƙi.

Jami'an Kurɗawa sun bayyana cewa an kashe farar hula a harer-haren sama inda mayaƙan yankin Peshmerga da dama suka mutu a wani hari da aka ɗora alhakinsa ga PKK.

Firaiminista Masrour Barzani ya dage kan cewa tafiyar da Kurɗawan Iraƙi ke yi ta baya-bayan nan zuwa Turai ba wai batun ci rani bane, amma lamarin safarar mutane, inda ya ce masu aikata laifi na amfani da ƴan ci ranin inda suka maƙale a tsakanin Belarus da Tarayyar Turai.