Bidiyo: Musulmai da Kiristoci na aiki tare wajen sake gina birnin Mosul na Iraƙi.

Bayanan bidiyo, Musulmai da Kiristoci na aiki tare wajen sake gina birnin Mosul na Iraƙi
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fiye da shekara bayan mummunan yaƙin sake ƙwato Mosul daga hannun ƙungiyar IS, har yanzu tsohon birnin a lalace yake.

An ɗauki mutane daga addinai daban-daban a birnin don yin aiki ƙarƙashin wani shiri mai taken “sake farfaɗo da Mosul”, kamar sake gina Masallacin Al Nuri da Cocin Al Saa and Al Tahira masu tsohon tarihi.

Fafaroma Francis ya shirya kai ziyara dukkan wurare ukun a watan Maris, amma a baya-bayan nan ya fara tababar zuwa, saboda damuwar kar a tara mutane a yayin da ake fama da annobar Covid-19.

Bidiyo daga Daisy Walsh da Gabriel Chaim.

Wasu bidiyo da za ku so ku kalla: