Sauyin yanayi: Amurka da China sun shammaci duniya

Shugaban Amurka Joe Biden na gaisawa da takwaransa na China Xi Jinping
Bayanan hoto, kasashen biyu sun yi alkawarin aiki da gaske domin daukar matakan da ake bukata kan matsalar sauyin yanayi
An wallafa

A wani mataki na ban mamaki, Amurka da China sun fitar da wata sanarwa ta hadin guiwa, wadda a ciki suke cewa za su kara kokari wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi tare.

Yayin da aka shiga kwanakin karshe a taron koli na duniya da ake yi a kan matsalar ta dumamar yanayi a Glasgow, kasashen biyu wadanda suka fi fitar da hayakin da ke haifar da matsalar sun ce ana bukatar matakin gaggawa da kuma gagarumin hadin kai a cikin shekara goma nan gaba domin cimma burin da ake so na shawo kan wannan matsala ta sauyin yanayi.

John Kerry

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wakilin Amurka a taron sauyin yanayi na duniya John Kerry ya ce lalle akwi bukatar hada kai

Sanarwar ta hadin guiwa da kasashen biyu suka fitar wadda ta zo da mamaki ganin irin takun sakar da ke tsakaninsu kan batutuwa da dama ciki har da batun na sauyin yanayi, tana kunshe ne da alkawari na daukar mataki na ceto duniya daga halin da take ciki a sabili da ayyukan dan adama da ke haifar da illolin da dumamar yanayin ke jawowa.

Kasashen biyu sun jaddada muhimmancin rage tazarar da ke akwai tsakanin abin da ake bukata.

Domin takaita karuwar dumin duniya zuwa tsakanin lamba daya da rabi zuw lamba biyu a ma'aunin selshiyas, da kuma ainahin abin da ake yi don tabbatar da raguwar, ba maganar baka ba kawai.

Da yake magana a wurin taron kolin a Glasgow, babban wakilin China a kan sauyin yanayin, Xie Zhenhua, tare da takwaransa na Amurka, John Kerry, sun ce matakin nasu ya nuna ta hadin kai ne kawai za a kai ga samun cigaba.

Xie Zhenhua

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Babban mai shiga tsakani na China kan sauyin yanayi Xie Zhenhua ya nuna cewa ta hadin kai ne za a iya samun biyan bukata kan matsalar yanayi

Sanarwar tasu ta biyo bayan kusan taruka talatin da aka yi ta yi ta intanet a tsawon wata goma, sannan kuma sanarwar ta saba da ikirarin da Shugaba Biden ya yi a makon da ya gabata cewa, Shugaba Xi Jinping, na China ya kaurace wa matsalar sauyin yanayin, ta hanyar kin halartar babban taron na Glasgow.

Babban jami'in Tarayyar Turai a kan yanayi, Frans Timmermans, ya yi maraba da sanarwar ta China da Amurka, inda ya ce, "Baya ga abin da take nufi ga taron sauyin yanayin, tana kuma da muhimmanci sosai ga duniya saboda, idan har Amurka da China, duk da sabanin da da ke tsakaninsu a kan sauran batutuwa, a yanzu sun nuna wannan batu ne da ya sha kan sauran batutuwa.

Wannan ya fi muhimmanci, abu ne da ya shafi dorewar rayuwar dan adam, wannnan zai taimaka sosai wajen ganin al'ummar duniya ta yarda cewa akwai bukatar mu dauki mataki a yanzu, kuma ba shakka wannan yana da tasiri mai kyau a kan tattaunawarmu a nan Glasgow.''

Frans Timmermans

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babban jami'in Tarayyar Turai a kan yanayi, Frans Timmermans, ya yi maraba da sanarwar ta China da Amurka

Wannan sanarwa ta hadin guiwa daga kasashen biyu, China da Amurka, wadanda su biyun suke da alhakin fitar da kashi 40 cikin dari na hayakin da ke haifar da sauyin yanayi a duniya, ta nuna hadin kai na ban mamaki a tsakaninsu.

Kuma ta kara nuna cewa ko China ba ta fito fili ta furta ba , lalle ta yarda cewa matsalar sauyin yanayi tana bukatar matakan gaggawa, kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin duniya ta tunkari matsalar