Abokan gogayyar Amurka na neman yi mata fintinkau - Biden

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargadin cewa Amurka na kan gargarar rasa matsayinta da aka santa da shi a duniya.

Mista Biden ɗin ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi domin tallata shirinsa na samar da manyan ayyuka da kuma walwalar jama'a inda Mista Biden ɗin ya ce manufofin nasa tamkar gyara ne da kuma ɓatawa, kuma duk waɗanda suka yi adawa da waɗannan manufofin to tamkar suna son yi wa ci gaban Amurka ƙafar ungulu ne.

Yayin da Shugaban ke lissafo yadda ƙidɗidiga ke nuna cewa Amurkan ta zama koma baya a cikin tsararrakinta, ta ɓangaren ilimi da ababen more rayuwa. Mista Biden ɗin ya ce saka hannun jari na gwamnati ya ƙarfafa jarin masu zaman kansu a duk tarihin Amurka kuma ana sake bukatar hakan a yanzu.

Ra'ayoyin jama'a na maraba da ayyukan Shugaba Biden din sai dai ƴan Republican na adawa da su.

Shugaba Biden ɗin ya bayyana cewa "abokan goggayarmu ba za su tsaya su zura ido su ga me za mu yi ba, suna ta zuba biliyoyin daloli domin samar da ababen more rayuwa da kuma horas da jama'a tsawon shekaru.

"Alal misali kamar China, na sha faɗa cewa China na amfani da hanyoyin da ba su dace ba domin wuce abokan gogayyarsu, amma ba nan zancen ya tsaya ba.

"Suna zuba jari domin ƙarfafa kansu. A cikin ƴan shekarun nan, China ta kashe kusan ninki uku kan samar da ababen more rayuwa daga tattalin arzikinta idan aka kwatanta da mu. Sau uku fa ake magana," in ji Shugaba Biden.

Da alama dai ƴan jam'iyyar Republican sun shaƙar da Mista Biden ganin yadda suke neman shuri da kudurorinsa na ayyuka na dala tiriliyan 1 da kuma na dala tiriliyan uku da rabi.

Yan jam'iyyar democrats dai na ganin cewa idan ba a amince da waɗannan kudurorin ba domin zuba wa Amurkawa ayyuka yadda ya kamata ba, akwai alamun cewa za su sha ƙasa a zaben wakilan ƙasar da za a yi a ƙarshen shekara mai zuwa