Dirar mikiya a gidan Mai Shari'a Mary Odili yunƙuri ne na halaka ta - Kotun koli

Mary Odili

Asalin hoton, Other

An wallafa

Kotun ƙolin Najeriya ta bayyana samamen da aka kai wa ɗaya daga cikin manyan alƙalanta Mary Odili a ranar Juma'a a matsayin "wata manufa ta yunƙurin halaka ta ko kuma yi mata lahani."

Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gudanarwar Kotun ƙolin Festus Akande ya fitar ta danganta farmakin da manufar yaƙi da halaka ta yana mai cewa "wasu ɗauke da makamai da ake tunanin jami'an tsaro daga hukumomin gwamnati daban-daban waɗanda da alama sun zo ne da nufin kashe wadda suke nema da sunan samun sammacin gudanar da bincike da ba shi da tushe."

A ranar Juma'a ne wasu jami'an tsaro suka yi wa gidan Mary Odili matar Peter Odili tsohon gwamnan jihar Rivers dirar mikiya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sanarwar ta ce "mun yi matuƙar baƙin ciki da mamakin wannan rashin wayewa da abin kunya da aka yi kan ma'aikaciyar shari'a da ba ta ji ba ta gani ba, wadda ta shafe shekaru da dama na rayuwarta tana yi wa kasarta hidima."

Hukumar EFCC da DSS da ministan shari'a dukkaninsu sun nesanta kansu daga kai samame gidan Mai shari'ar.

Bayan ta yi Allah wadai, Kotun Kolin ta danganta farmakin da irin wanda ta ce jami'an tsaron farin kaya sun taɓa kai wa gidajen wasu alƙalai ciki har da nata guda biyu a Abuja a shekarar 2016.

Jami'an tsaro da suka kunshi ƴan sanda ne suka ka yi dirar mikiya gidan Misis Odili, bayan samun umarnin kotu domin gudanar da bincike kan bayanan da aka kwarmata masu cewa ana gudanar da ayyukan da ba su dace ba a gidan.

Kotun ta ce, kasancewar ɓangaren shari'a ɓangare ne na uku na gwamnati, ya kamata a dinga mutunta alƙalanta.

Tun da farko majalisar tarayyar kasar ta ɓukaci a gudanar da bincike kan al'amarin.

Kotun ƙoli ma a cikin sanarwar ta ce ta ƙaddamar da bincike tare da yin kira ga sufeto-janar na ƴan sanda da ya binciki farmakin da aka kai gidan Mary Odili tare da bayyana sakamakon binciken.