Barca ta fasa zawarcin Pogba, PSG za ta sayo Lewandowski

An wallafa

Da kyar ne idan Barcelona za ta yi zawarcin dan kwallon Manchester United, Paul Pogba, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar badi, domin ba za ta iya biyan albashin dan wasan mai shekara 28 ba. (AS)

Burnley na bibiyar dan kwallon tawagar Ingila mai taka leda a Chelsea, Ross Barkley da take son dauka a watan Janairu. (Sun)

Arsenal za ta taya dan kwallon Real Madrid da tawagar Wales, Gareth Bale a cikin watan Janairu. (Defensa Central - in Spanish)

Paris St-Germain za ta yi kokarin sayo ko dai dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ko dan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland, domin maye gurbin Kylian Mbappe ko da zai koma Real Madrid a badi. (Le 10 Sport)

Mai wakiltar mai tsaron bayan Juventus, Matthijs de Ligt wato Mino Raiola ya yi wa Manchester City da kuma Chelsea tayin dan kwallon mai shekara 22 idan suna bukata. (Calciomercato - in Italian)

Wakilin dan kwallon Sifaniya, Ansu Fati ya dakatar da tattaunawa kan batun tsawaita yarjejeniyar ci gaba da wasa a Barcelona, bayan da Jorge Mendes ke bukatar karin kaka biyu gad an wasan mai shekara 18 ya yi watsi da Yuro biliyan daya da Barcelona ta gindaya kudin sayensa idan kwantiraginsa bai kare a Camp Nou ba. (El Nacional - in Catalan)

Tottenham Hotspur da kuma Newcastle United na bibiyar kwallon dan wasan Fiorentina, Dusan Vlahovic, mai shekara 21. (Sun)

Ita kuwa Aston Villana son daukar dan wasan Bologna, Aaron Hickey, wanda ke taka rawar gani a Serie A ta bana. (Sun)

Manchester United ba za ta kori Ole Gunnar Solskjaer ba duk da cin wasa hudu daga karawa takwas Premier League ta bana. (The Athletic)

Arsenal da kuma Leicester City na bibiyar dan kwallon Southampton, Mohamed Elyounoussi, mai shekara 27. (Team Talk)