Kasuwar 'yan wasa: Makomar Pogba, Haaland, Olmo, Lingard, Bailly, Tchouameni

An wallafa

Barcelona na shirin taya dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21 da tauraron Faransa Paul Pogba, dan Manchester United mai shekara 28 da kuma gwanin dan wasan Sifaniya Dani Olmo, mai shekara 23. (Mundo Deportivo )

Sai dai yayin da kwantiragin Pogba zai kare da Manchester United a bazara ta gaba, kungiyar na shirin kara wa dan wasan albashi ya rika daukar fam dubu 400 a duk mako, abin da zai sa ya zama mai daukar albashi mafi yawa a tarihin Premier. (Express)

Dan wasan tsakiya Jesse Lingard, mai shekara 28, da dan baya Eric Bailly, mai shekara 27, na daga cikin 'yan wasa bakwai da watakila Manchester United za ta sayar da su a tankade da rerayar da za ta yi a watan Janairu. (Sun)

Chelsea za ta yi gogayya da Juventus wajen zawarcin matashin dan wasan tsakiya na Monaco Aurelien Tchouameni, dan Faransa mai shekara 21, a watan Janairu. (Tuttomercatoweb)

Liverpool da Tottenham da Juventus na shirin fafatawa a kan dan wasan gaba na gefe na Bayern Munich da Faransa Kingsley Coman, mai shekara 25. (Fichajes)

Chelsea ma na sha'awar Coman bayan da tsohon darektan wasanni na Bayern Munich ya ba shi shawarar barin kungiyar. (Mirror)

Kociyan Barcelona Ronald Koeman bai san makomarsa ba yayin da rahotanni ke cewa shugaban kungiyar Joan Laporta na hada sunayen wadanda yake ganin za su maye gurbinsa. (Express)

Watakila dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, mai shekara 28, har yanzu yana damuwa da rashin tafiyarsa Manchester City a bazaran nan. (TalkSport)

Juventus ta yi shirin daukar Gianluigi Donnarumma, mai shekara 22, daga AC Milan a matsayin wanda ba shi da wani kwantiragi a kansa a bazaran nan, amma ta janye saboda matsalar rashin kudi ta bar Paris St-Germain ta janye shi. (Goal)

Darektan wasannin PSG Leonardo ya yi watsi da rahotannin da ake yadawa cewa Lionel Messi, mai shekara 34, zai rika samun sama da fam miliyan 30 a shekara a tsawon kwantiragin shekara ukun da zai yi.(Mail)

Manchester United na tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, a kan sabon kwantiragi. Bruno Fernandes da Luke Shaw ma na daga jerin 'yan wasan da za ta sabunta wa kwantiragi. (Fabrizio Romano)

Arsenal ta ware fam miliyan 20 domin taya dan wasan gefe na gaba na tawagar Holland ta 'yan kasa da shekara 21 da kungiyar Club Bruges Noa Lang,mai shekara 22. (Fichajes daga Mirror)