Yadda Fitattun mata a Najeriya suka yi raddi kan yadda suka ce ana tsangwamar rayuwarsu

Asalin hoton, BBC/INSTAGRAM
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Wasu mata a Najeriya ciki har da fitattun mutane sun karaɗe shafin Instagram da Facebook suna tsokaci kan irin tsangwama da kalaman cin zarafi da suka fuskanta a rayuwarsu.
Matan da ke tsokaci ta hanyar amfani da wani maudu'in '#NobodyLikeWoman' da suka kirkira na magana ne kan irin sa ido da gorin rayuwa da ake masu a lokuta daban-daban na rayuwarsu.
Matan wanda galibi masu fitowa ne a fina-finan da wadanda suka shahara ko ke da karfin fada aji, na bayyana tsananin rayuwa da ya mace ke karo da su a lokacin gudanar da al'amuran yau da kullum.
Wannan maudu'i ya soma jan hankali ne lokacin da mawaƙiyar Najeriya, Simi ta soma jagorantar maudu'in da ta wallafa hotunan mata dauke da bayanai masu zafi da nuna ɓacin rai da suka fuskanta a rayuwarsu, kan aure ko aiki da yanayin halitta.
An yi amfani da maudu'in sama da sau 10,000 a shafin Instagram, sannan a Facebook sama da mutum dubu biyar sun yi amfani da maudu'in wajen bayar da labarinsu.
Me suke cewa?
Galibi dai masu tsokaci sun bayar da wani labarin da ba za su taɓa mantawa da shi ba ko wani gori ko tsangawama da suka ci karo da su.
Shahararriyar mai fitowa a shirin Nollywood Adesua Etomi-Wellington ta wallafa nata labarin da ke cewa: "Har yanzu ba ta ɗau ciki ba?"
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1
Mai fitowa a fina-finai kuma mai tallata kayan kawa, Efe Irele ta wallafa nata hoton da ke cewa: "Za mu share ɗare muna naɗar fim. Ba wai kina da miji ba ne ko yara da ke jiranki a gida."
Maudu'in ya ja hakali har zuwa sauran fitattun mutane da ke zaune a kasashen ketare, inda ake samun karin mutane da ke fitowa suna shaida irin banbamci ko tsangwama da mace a Najeriya ke fuskanta.
Wata mata mai suna - Lateefah Jim - ta rubuta a shafinta na Instagram cewa: "Na ga wannan maudu'in kuma ya sosa mu rai. A koda yaushe batun na mata ne. Mara aure (babu wanda ke son aurenta), bazawara (ta kashe aurenta), mara ɗa (juyace) ko wacce mijinta ya mutu (farar ƙafa gareta) #nobodylikewoman."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2
Sauran mata da suka bi sahu na cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 3
"Na sha jin batutuwa marasa dadi kan aure, gwara ki sayar kawai, ki sayar da shagonki ya fiye girma, za ki tsorata maza, Maza ba sa son mata masu dogon buri, ki rage girman kai, ko yaya ki dage ki yi aure."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 4
Vanney_gold ta ce: "Babu mai aurenta, maza ba sa son mata masu kiɓa, ba ta da makoma ma saboda ba ta da ilimi."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 5
Karin haske
Batun tsangwamar mata abu ne da ya jima ana yawaita samun ce-ce-ku-ce, kuma so tari mata na yawaita korafi wajen kare hakkinsu kan wasu kalamai na kaskantarwa da ake amfani da shi a kansu.
Kirkirar wannan maudu'i da ganin yadda yake jan hankali na nuna karara irin damuwar da mata ke ciki a kowanne ɓangare na rayuwa.
Irin waɗannan matsaloli ya sa a galibin lokuta ake samun masu fitowa domin yaƙar wasu dabi'u da suke ganin na tasiri ko sare gwiwar mata da dama.
Wani abin takaici da galibin matan ke tabowa ko magana a kai na nuna irin matsi ko yanayi na akuba da suka taba shiga a rayuwarsu.
A kasan kowanne hoto da aka wallafa dauke da maudu'i ana samun tarin tsokaci masu sosa rai kan irin kalubale ko kalaman tsangwama da kowace mace ta fuskanta a lokacin gudanar da lamuranta na rayuwa.