Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trent Alexander-Arnold ba zai buga wasan Man City ba
Trent Alexander-Arnold ba zai yi wa Liverpool karawar Premier League da za ta yi da Manchester City ranar Asabar ba, in ji Jurgen Kloop.
Liverpool ce za ta karbi bakuncin City a wasan mako na bakwai a babar gasar ingila a Anfield.
Mai shekara 22 bai je karawar da Liverpool ta casa Porto 5-1 a gasar Champions Legue ba ranar Talata, sakamakon jinyar da yake yi.
Haka kuma matashin ba zai buga wa Ingila wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta fafata da Andorra da kuma Hungary.
Klopp na sa ran Alexander-Arnold zai koma taka leda, bayan wasannin shiga gasar cin kofin duniya tare da Thiago Alcantara, wanda ke jinya.
Liverpool, wadda ta tashi 3-3 a gidan Brentford a Premier league a makon jinya tana ta daya a kan teburi da maki 14.
City kuwa wadda ta je ta ci Chelsea a Stamford Bridge tana ta biyu a teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool.
Ranar Laraba City ta yi rashin nasara a gidan Paris St Germain da ci 2-0 a wasa na bibiyu na cikin rukuni a Champions League.