'Yan matan da suke yin mutum-mutumi a Afghanistan sun samu mafaka a Mexico

Ministan harkokin wajen Mexico Marcelo Ebrad lokacin da ya karbi 'yan matan...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ministan harkokin wajen Mexico Marcelo Ebrad lokacin da ya karbi 'yan matan
An wallafa

A baya, ana yi wa wata gamayyar mata matasa 'yan Afghanistan da ke ƙera mutum mutumi kallon kyakkyawar makomar kasar.

Matasa ne su 20 'yan tsakanin shekaru 13 zuwa 18 waɗanda suka kafa ƙungiyar mata zalla ta farko da ke ƙera kayan fasahar zamani a ƙasar da babu abin da ya ɗaɗata da ƙasa da 'yancin mata, ballantana kuma bunƙasar harkar fasahar kimiyya.

To sai dai dawowar Taliban kan mulki cikin hanzari a ranar 15 ga Agusta ta sanya duk nasarorin da suka samu cikin hadari.

Kungiyar ta tauye wa mata hakkokinsu na yin aiki da karatu a karo na ƙarshe da suka jagoranci kasar a shekarun 1990.

Tun daga wannan lokacin, burin mutane da dama kamar wadannan 'yan mata ya gamu da cikas.

Bayan karɓar mulkin na Taliban a yanzu, sun yanke shawara mai tsauri ta barin ƙasarsu da neman mafaka a ƙasashen waje, suna tsoron zaluncin Taliban da ramuwar gayya.

Don haka bayan ƙetare ƙasashe shida da kewaya kewaye a cikin teku, matasan matan biyar waɗanda da farko suka kafa ƙungiyar, da suka hadar da (Fatemah Qaderyan, da Lida Azizi, da Kawsar Roshan, da Maryam Roshan da Saghar Salehi) sun sami mafaka ta wucin gadi a Mexico ranar Talata da ta gabata.

'Daidaiton jinsi'

'Yan matan na cikin wani babban gungun ƴan gudun hijirar Afghanistan da za su isa Mexico da sauran kasashen Latin Amurka a cikin kwanaki masu zuwa.

"Sun ja hankalin duniya ƙwarai da gaske, kuma mutane da dama sun tsaya su ga makomarsu', muna musu maraba' in ji Ministan Harkokin Wajen Mexico Marcelo Ebrard, a wani saƙo da ya wallafa a Tuwita.

Afghan asylum seekers at their arrival in Mexico

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mexico ta kuma bai da mafaka ga ƴan jarida da iyalansu da dama ƴan Afghanistan

A cewar gwamnatin Mexico, 'yan matan sun samu biza ta jin ƙai, wadda za ta ba su damar zama a kasar na akalla watanni shida, tare da yiwuwar tsawaitawa.

Za su kuma sami masauki da abinci kyauta tare da taimakon kungiyoyi daban-daban.

Yayin da wasu ke yabon wannan yunƙuri, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun soki gwamnatin kasar kan kyakkyawar tarbar da aka yi wa 'yan matan na Afganistan, saboda ta bambanta da kulawar da ake bai wa' yan ci -rani a kan iyakar Mexico da Amurka, inda galibi ake mayar da bakin haure zuwa ƙasashensu na asali.

Yayin da wasu da yawa ke cewa an ci zarafinsu, ko an zalunce su, baya ga sanya su cikin uƙuba.

Su wanene 'yan matan?

Wani hamshakin dan kasuwa Roya Mahboob da ke gudanar da Asusun Citizen Digital ne ya hada 'yan mata wuri guda a matsayin kungiya.

Yana jagorantar kungiyar mai zaman kanta ta Amurka wacce ke taimaka wa 'yan mata da mata a ƙasashe masu tasowa samun damar yin amfani da fasaha kuma tana ba da darussa a fannoni kamar kimiyya, injiniya, lissafi da fasahar ƙere-ƙere.

The "Afghan Dreamers" during the 2017 International Robotics Championship

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 2017 kungiyar 'yan matan da ta shiga fitacciyar gasar ƙasa da ƙasa ta mutum-mutumi

A Afghanistan, aikin bunkasa kimiyyar ya fi ƙarfi a Herat, yammacin ƙasar, don haɓaka kimiyya da ƙarfafa 'yan matan Afghanistan a cikin ƙasa inda rawar mata ta taƙaita ga gida a lokacin mulkin Taliban na baya (1996-2001).

Jim kadan bayan ƙirƙirar kungiyar, a cikin 2017, matasan sun fara samun kulawar kasa da kasa lokacin da suka lashe lambar yabo ta musamman a Gasar ƙere-ƙere ta Duniya da aka gudanar a Washington DC.

Kyautar tasu abar mamaki ce ba wai kawai saboda sun kasance matasa ne da suka fito daga ƙasar da mata ba su da 'yanci ba, har ma da irin fasahar da Ubangiji ya huwace musu.

Bayan an karbe su su shiga gasar a karon farko da wasu suka samu wannan dama daga Afghanistan, sun yi tafiyar tsawon kilomita 800 daga garinsu da ke Herat zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Kabul.

One of the Afghan team members at the 2017 International Robotics Championship shows her medal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...kuma sun samu kyauta ta musamman a gasar

A lokacin da suka isa sai aka hana su izinin shiga, wato biza. Suka sauke gwadawa aka sake hana su.

Sai da Shugaba Turmp ya shiga lamarin sannan suka samu damar shiga, sai dai shigar tasu ba ita ce karshen harkokinsu ba.

Jim kaan kafin tafiyarsu zuwa Washington, gwamnatin Afghanistan ta kwace kayayyakin da suka tsara yin amfani da su a wajen gasar

Bayan da 'yan matan suka isa Washington, sai hankalin dukkan kafafen yada labaran Amurka ya koma kansu duk da fadi tashin da suka yi fama da shi a tafiyar.

Yaki da cutar korona

Bayan wannan, matasan 'yan kasa da shekara 20 sun kuma samu shahara a Afghanistan.

Lokacin da annobar korona ta barke a shekarar da ta gabata, sun hadu wuri guda tare da wasu likitoci, da injiniyoyi, da 'yan boko don kokarin gano hanyoyin kawo karshen wannan kalubale.

Herat na ta fama da karancin na'urorin taimaka wa numfashi.

An "Afghan Dreamer" is seen assembling a respirator

Asalin hoton, The Digital Citizen Fund

Bayanan hoto, : Kungiyar "Afghan Dreamers" ta yi amfani da iliminsu wajen taimakawa da kera na'urorin taimaka wa numfashi ga masu fama da cutar korona a Afghanistan

Kungiyar matasan ta "Afghan Dreamers" sun bullo da wani aiki don kera na'urorin taimaka wa numfashin ta hanyar amfani da samfurin irin wanda da injiniyoyin Makarantar Fasaha ta Massachusetts suka kera da kuma wasu kayyakin jikin motoci.

Bayan samun izuni daga kwararrun daga Amurka na amfani da samfurin, sun zage damtsensu wurin fara aikin.

'Yan matan da dama na gudanar da aikin a yayin da kuma suke azumi saboda a lokacin watan Ramadan ne, wanda a cikinsa duka Musulmai bas a cin abinci sai bayan faduwar rana.

Matakan bayar da tazara ma ya tilsata musu gudanar da aiki mutum daya kowa zai yi shi kadai.

Wasu ma su kan hadu a karon farko ne lokacin hadawa wanda kowa zai fito a yi aiki tare - kana ''dreamers'' da dama sun kamu da cutar korona.

Tserewa

Kungiyar ta "Afghan Dreamers" an san da zaman su a kasashen duniya da kuma cikin gida, ta kuma bunkasa a yawan mambobi da suka hada da 'yan matan da aka haifa bayan shekarar 2001, lokacin da dakarun da Amurka ta jagoranta suka fatattaki kungiyar Taliban bayan hare-haren 9 ga watan Satumba.

An "Afghan Dreamer" is seen during a press conference in Mexico City

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, "Ba rayuwarmu kadai suka ceto ba, har ma da burin da muke da shin a rayuwa,'' 'yan matan suka bayyana game da matakin da mahukuntan kasar Mexico suka dauka na samar musu da mafaka.

Bayan dawowar kungiyar masu rajin tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci kan mulki 'yan matan na fargabar mummunan martani.

Bayan yunkuri da dama na barin kasar, tara daga cikin mambobin sun yi nasarar tserewa zuwa kasar Qatar da taimakon asusun tallafi na Digital Citizen Fund.

"Lokacin da muka ji cewa za a kwace birnin Kabul, mun samu yin magana da ma'aikatar harkokin wajen Qatari, kuma ba tare da bata lokaci ba suka fara shirya mana takardun visa don ficewa da su,'' wata babbar jami'a a asusun tallafi na Digital Citizen Fund Elizabeth Schaeffer Brown ta shaida wa BBC.

A can ne suka gano cewa kasar Mexico ta amince da bukatarsu ta zama masu neman mafaka.

"Ba rayuwarmu kawai suka ceto ba, har ma da burin da muke da shin a rayuwa, burin da muke ta fatan ya cika,'' 'yanmatan suka bayyana a wani taron manema labarai bayan da suka isa birnin Mexico.

'Labarinmu ba zai yi mummunan karshe ba'

Sun bayyana cewa tun bayan da Taliban ta kwace mulki, halin da aka shiga ya zamar musu ''tamkar juyin waina'' - babu sauki a gare su.

"A wannan mulki, mu 'yanmata muna cikin matsaloli (...) shi yasa muke matukar jin dadin kasancewa a nan."

Matasan na "dreamers" sun kuma ce a karkashin tsarin mulkin Taliban na shari'ar Musulunci, zai yi matukar wahala a garesu su cigaba da mayar da hankulansu wajen ilimin kimiyya.

"Labarinmu ba zai kasance mai mummunan karshe ba,'' 'yanmatan suka bayyana.

Kamar yadda wasu rahotannin kafafan yada labarai suka bayyana, 'yanmatan sun riga sun samu tallafin karatu daga jami'oi da dama na Amurka.