Kasuwar 'yan kwallo: Raphael Varane, Saul Niguez, Erik Lamela, Koulibaly

An wallafa

Paris St-Germain ta tattauna da wakilin Kalidou Koulibaly dan bayan Senegal da Napoli mai shekara 30 a kokarin kungiyar na sayensa. (Corriere dello Sport)

Watakila Newcastle ta karkata ga dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Ross Barkley, mai shekara 27, idan ta kasa samun Joe Willock mai shekara 21 shi ma dan Ingila daga Arsenal. (The Athletic)

Manchester United na dab da cimma yarjejeniya da Real Madrid ta sayen dan bayan Faransa Raphael Varane, mai shekara 28, a kan kusan fam miliyan 42. (Jaridar Marca)

Haka kuma United na ganin za ta iya kammala sayen dan wasan tsakiya na Sifaniya Saul Niguez daga zakarun La Liga Atletico Madrid a kan kusan fam miliyan 45. Ana kuma danganta dan wasan mai shekara 26 da Barcelona da Juventus. (Jaridar Mail)

Borussia Dortmund na nuna cewa ta kammala komai domin sayen dan wasan da Liverpool ke hari, Donyell Malen mai shekara 22 a kan fam miliyan 26.

Kungiyar ta Jamus tana daukar dan wasan gaban na PSV Eindhoven da Holland a matsayin wanda zai maye gurbin, Jadon Sancho na Ingila, mai shekara 21, wanda Manchester United ta saya. (Jaridar Fabrizio Romano)

Dan wasan gaba na gefe dan Argentina Erik Lamela, mai shekara 29, na dab da kammala tafiyarsa daga Tottenham zuwa Sevilla, yayin da dan wasan gaba na gefe na Sifaniya Bryan Gil, mai shekara 20, zai bar Sevillan shi kuma ya koma Tottenham. (Jaridar Marca)

Juventus ta shirya yin sabuwar tattaunawa da kungiyar Sassuolo a kokarinta na ganin ta sayi dan wasan tsakiya na Italiya Manuel Locatelli, wanda ake dangantawa da tafiya Arsenal. (Goal)

Real Madrid ba za ta sabunta kwantiragin dan wasanta na Sifaniya, Isco mai shekara 29 ba. Yarjejeniyar zamansa a kungiyar za ta kare ne a bazara ta gaba. (AS)

Dan wasan tsakiya na Leicester City Hamza Choudhury, mai shekara 23, yana neman kungiyarsa ta bayar da shi aro ga Newcastle. Tsohon dan wasan na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, na ganin hakan a matsayin wata dama da zai samu yin wasa yadda yake so akai akai. (Northern Echo)

Dan wasan tsakiya na Chelsea da tawagar Scotland Billy Gilmour, mai shekara 20, ya nuna wata baiwar da yake da ita ta daban da taka leda, inda ya rera wata waka a wata mashaya a Norwich, inda yake zaman aro a yanzu. (Jaridar Sun)