Rangers ta doke Real a wasan sada zumunta a Glasgow

An wallafa

Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Rangers da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka kara a filin wasa na Ibrox ranar Lahadi.

Kungiyar Sifaniya ce ta fara cin kwallo ta hannun Rodrygo, daga baya Rangers ta farke ta hannun Fashion Sakala, sannan Cedric Itten ya kara na biyu.

Wannan shine wasa na uku na sada zumunta da Real ta yi don tunkakar kakar bana da za a fara cikin watan Agusta.

Real ta yi wasan sada zumunta na farko ba 'yan kallo da Fuenlabrada sannan ta kece raini da Rayo Vallecano,

Wannan wasan na sada zumunta daya ne daga bikin da Rangers ke yi na kusan cika shekara 150 da kafuwa.

Rangers din karkashin Steven Gerrard ita ce ta lashe kofin gasar Scotland a kakar da ta wuce, kuma ba a doke ta ba a karawa 38 da ta yi a wasannin.

Wannan nasarar da Rangers ta yi na nufin watakila ta kara taka rawar gani a kakar da za a fara, ita kuwa Real Madrid sai ta kara sa kwazo idan tana son yin abin azo a gani.

Real Madrid za ta fara buga La Liga ta bana a gidan Deportivo Alaves cikin watan Agusta.