Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Federico Chiesa, Joaquin Correa, Anthony Martial, Paul Pogba

An wallafa

Juventus ta yi watsi da tayin fam miliyan 86 da Liverpool ta yi wa Federico Chiesa. Dan wasan gaban na gefe mai shekara 23, ya taka wa Italiya leda a gasar cin kofin Turai da aka yi, Euro 2020. (Jaridar Repubblica)

Arsenal da Tottenham da kuma Everton, dukkaninsu na duba yuwuwar zawarcin dan gaban Argentina Joaquin Correa, mai shekara 26,wanda ake sa ran zai bar Lazio a bazaran nan. (Corriere dello Sport)

Watakila Manchester United ta nemi sayar da Anthony Martial, mai shekara 25, da Tottenham ke sha'awar dan gaban dan Faransa. (Jaridar Star)

Shi kuwa kociyan United Ole Gunnar Solskjaer yana son Paul Pogba, mai shekara 28, ya tsaya a kungiyar ne, yayin da Paris St-Germain ke son dan wasan tsakiyar na Faransa. (Manchester Evening News)

Sabon dan wasan tsakiya na PSG dan Holland Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, ya ce ya ga lalle ba a kaunarsa an kuma ware shi ana suka da nuna masa tsana a shafukan intanet kafin tafiyarsa daga Liverpool a watan Yuni. (Jaridar Observer)

Kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 27, ba zai samu damar fara wasan gasar Premier ba saboda gajiyar da ya yi a gasar cin kofin Turai da aka kamala. Dan gaban na Tottenham na son tafiya Manchester City.(Jaridar Telegraph)

Arsenal na fatan tabbatar da sayen dan bayan Brighton, dan Ingila Ben White mai shekara 23 a kan fam miliyan 50, bayan kammala gwajin lafiyarsa a karshen makon nan. (Jaridar Mail)

Haka kuma Gunners na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya dan Switzerland Denis Zakaria, mai shekara 24, wanda ya bayyana aniyarsa ta barin Borussia Monchengladbach. (Jaridar Mirror)

Crystal Palace ta kusa cimma yarjejeniyar sayen dan bayan Lyon, dan Denmark, Joachim Andersen, mai shekara 25 a kan fam miliyan 20, sannan kuma tana ci gaba da tattunawa don sayen dan bayan Schalke da Turkiyya Ozan Kabak, mai shekara 21. (Jaridar Mail)

Blackburn ta yi watsi da tayin da Watford ta yi na fam miliyan 15 a kan Adam Armstrong, mai shekara 24, inda ta kafe sai an biya fam miliyan 25 a kan tsohon dan gaban na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21. (Jaridar Sun)

An sauya sunan kyaftin din Watford mafi dadewa Troy Deeney, mai shekara 33, zuwa 'Tom Deeney' a takardar jerin sunayen 'yan wasan da za su yi wasan sada zumunta ranar Asabar da West Brom. (Jaridar Sun)