Afghanistan: Wakilan gwamnatai da na Taliban za su gana

Ana ganin ganawa gaba da gaba tsakanin wakilan gwamnatin Afghanistan da shugabannin Taliban alama ce mai kyau

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana ganin ganawa gaba da gaba tsakanin wakilan gwamnatin Afghanistan da shugabannin Taliban alama ce mai kyau
An wallafa

Wata tawaga mai karfin gaske ta shugabannin siyasar Afghanistan ta nufi Qatar, domin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya, yayin da Taliban ke ci gaba da kama sassan kasar.

Samar da tawagar karkashin jagorancin shugaban babbar majalisar sasantawa ta kasar Dakta Abdullah Abdullah, wani yunkuri ne na gaggauta farfado da tattaunawar da ta dade da tsayawa yayin da tashin hankali ke kara kazanta.

A wata hira da ya yi da BBC kafin tashinsa, jagoran tawagar Dakta Abdullah Abdulah, ya ce ba tabbas za a samu gagarumar nasara, amma tattaunawar baya-bayan nan ta yi armashi, kuma yanzu an kara samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Al'ummomi da dama na Afghanistan ba su san zaman lafiya ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Al'ummomi da dama na Afghanistan ba su san zaman lafiya ba

Tun a watan Satumba ne ake ta tattaunawa bayan tattaunawa, ba tare da cimma wata gagarumar nasara ba ta ganin karshe ko akalla samo bakin zaren tabbatar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu na Taliban da kuma shugabannin siyasa ko kasar ta Afghanistan.

Wannan babbar tawagar ta yanzu da za ta nufi Qatar daga babban birnin kasar, Kabul, wadda ta kunshi shugabannin siyasa irin su, tsohon shugaban kasar Hamid Karzai, za ta yi kokarin rage katafaren bambancin da ke tsakanin bangarorin biyu ne.

Sai dai kuma har yanzu, akwai bambanci sosai a tsakanin bangarorin kan kusan dukkanin batutuwa kama daga sabon tsarin siyasar da za a bi zuwa tsarin mulki na Musulunci.

Ana ganin babu makawa, nasarar da Taliban ke samu a yanzu bayan dar sojojin Amurka suka fara ficewa, da hakan ke kara musu karfi, za ta sa kungiyar tsananta bukatunta.

Fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Taliban ya kara tsananta tun bayan da sojojin Amurka suka fara ficewa daga Afghanistan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Fada tsakanin dakarun gwamnati da Taliban ya tsananta tun bayan da sojojin Amurka suka fara ficewa, ficewar da za su kammala 11 ga Satumba

A kwanan nan Taliban ta yi ikirarin cewa mayakanta sun sake kama kashi 85 cikin dari na kasar, abin da babu wata kafa mai zaman kanta da za ta iya tabbatar da sahihancinsa, wanda kuma daman gwamnati ta musanta.

Sai dai wasu rahotanni na cewa Taliban din na rike da sama da kashi daya bisa uku na larduna 400 na kasar.

Taliban din dai a baya bayan nan ta gabatar da shawarar dakatar da bude wuta tsawon wata uku a Afghanistan din, idan za a saki mayakanta 7,000, kamar yadda wani jamiin gwamnati ya fada.

A shekarar da ta wuce mayakan kungiyar 5000 da aka saki, ana ganin yawancinsu sun sake komawa filin daga, lamarin da ya kara tashin hankalin.

Sai dai daya daga cikin masu shiga Tsakani na bangaren gwamnati Nader Nadery, ya bayyana bukatar da cewa babba ce, amma dai gwamnati ba ta bayyana yadda za ta amsa ta ba.

Dukkanin bangarorin biyu - tawagar da kuma 'yan Taliban na fuskantar matsin lamba daga 'yan kasar da kuma kawayen Afghanistan din na ganin sun kawo karshen wahala da rashin tabbas da kasar ke ciki yayin da yakin ke kara zafafa.