Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Haaland, Guardiola, Richarlison, Jorginho, Ramos, Goretzka, Sabitzer

Erling Braut Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyoyi da yawa sun so sayen Erling Braut Haaland
An wallafa

A shirye Chelsea take ta bayar da fam miliyan 150 a kan dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland kuma tuni har ma kungiyar ta Stamford Bridge ta tattauna da bangaren dan wasan na kasar Norway mai shekara 20. (90 Min)

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya ce kungiyar ba za ta iya sayen wani dan wasan gaba ba a yanzu a irin farashin da ake sanya wa 'yan wasa, kuma bisa ga dukkan alamu Zakarun na Premier ba za su sayi wani dan gaba ba. (TVS, via Mail)

Kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti ya gaya wa kungiyar cewa yana son dauko dan wasan gaba na Brazil Richarlison, mai shekara 24, daga tsohuwar kungiyarsa Everton, kuma kungiyar ta La Liga za ta dubu ta ga idan cinikin zai yiwu. (ESPN)

Richarlison

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ancelotti na son Richarlison ya bi shi Real Madrid

Wakilin dan wasan tsakiya na Chelsea Jorginho ya ce wasu kungiyoyi sun nuna sha'awarsu a kan dan wasan na tawagar Italiya mai shekara 29, amma kuma shi yana sha'awar tattaunawa da Chelsea don tsawaita zamansa a kungiyar har bayan kwantiraginsa na 2023. (Radio Marte, via Metro)

Za a iya sayar da kyaftin din RB Leipzig Marcel Sabitzer, mai shekara 27, a kan fam miliyan 17, yayin da tattaunawa kan sabon kwantiragin dan wasan na tsakiya na Austria da yake shiga watanni 12 na karshe na kwantiraginsa ke cin tura. (90 Min)

Paris St-Germain ta yi kuskuren tabbatar da labarin sayen dan bayan Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 35, wanda ya bar Real Madrid bayan karewar kwantiraginsa,inda ta wallafa labarin a shafinta na intanet tun kafin fitar da sanarwa a hukumance ta kamala cinikin, wadda ake sa rai Alhamis din nan. (Goal)

Sergio Ramos ya bar Real Madrid bayan shekara 16 inda ya dauki kofi 22

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sergio Ramos ya bar Real Madrid bayan shekara 16 inda ya dauki kofi 22

Wolves ta amince ta sayar wa Sporting Lisbon dan bayanta na kasar Portugal Ruben Vinagre mai shekara 22 a kan fam miliyan 8 da dubu 600. (Football Insider)

Tottenham na sa ido a kan dan bayan Sassuolo Mert Muldur, mai shekara 22, wanda kuma West Ham ma aka ce tana sha'awar dan wasan na tawagar Turkiyy. (Mail)

Southampton na da kwarin guiwa kan sayen dan wasan gaba, dan Ingila, Adam Armstrong, mai shekara 24, daga Blackburn Rovers a kan fam miliyan 10 da sauran 'yan tsarabe-tsarabe. (Football League World)

Middlesbrough ta yi nisa a tattaunawar da take yi kan sayen dan wasan tsakiya na Atletico Banfield, Martin Payero, mai shekara 22, wanda Argentina ta sa sunansa cikin 'yan wasan da za ta je gasar Olympics a Tokyo da su, a bazaran nan.(Football Insider)

Kociyan Bayern Munich Julian Nagelsmann ya ce dan wasan tsakiya na tawagar Jamus Leon Goretzka, mai shekara 26, da ake danganta shi da tafiya Manchester United, dan wasa ne mai matukar muhimmanci ga kungiyar, kuma zai so ya ci gaba da aiki da shi tsawon shekaru. (Goal)

Franck Kessie ya koma AC Milan a 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Franck Kessie ya koma AC Milan a 2017

AC Milan za ta kara wa dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie mai shekara 24 albashi domin shawo kansa ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar. (Gazzetta dello Sport)

Dan bayan Italiya Davide Calabria, mai shekara 24, ya amince da sabon kwantiragi da AC Milan har zuwa 2025. (Calciomercato, daga Football Italia)