Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Sterling, Bale, Rogers, Tapsoba, White, Williams, Hennessey, Griezmann, Umtiti da sauransu

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Raheem Sterling ya dauki manyan kofuna bakwai da Manchester City tun da ya koma can daga Liverpool a 2015
An wallafa

Dan wasan Manchester City da Ingila Raheem Sterling ya nuna cewa a shirye yake ya bar kungiyarsa. Sai dai kociyansa Pep Guardiola yana son dan wasan na gaba na gefe mai shekara 26 ya ci gaba da zama a Etihad, duk da sha'awarsa da Real Madrid ke yi. (Jaridar Athletic)

Watakila Gareth Bale, mai shekara 31, ya yi ritaya daga taka leda a wata kungiya da zarar kwantiraginsa da Real Madrid, wadda ke ba shi albashin fan dubu 600 a sati ya kare a bazara mai zuwa. Ana ta rade-radi a kan makomar dan wasan na Wales bayan da ya koma Madrid daga zaman aro da ya je tsohuwar kungiyarsa, Tottenham. (Jaridar Mail)

Gareth Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham a lokacin a matsayin mafi tsada a tarihi a duniya - fam miliyan 85 a 2013

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gareth Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham a lokacin a matsayin mafi tsada a tarihi a duniya - fam miliyan 85 a 2013

Crystal Palace ta fara tattaunawa domin sayo dan wasan gaba na Manchester City dan Ingila Morgan Rogers, mai shekara 18. Hakan ya biyo bayan matakin da sabon kociyan kungiyar Patrick Vieira ke dauka na kokarin zuba matasa a kungiyar a bazaran nan. (Jaridar Mail)

Dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 25, yana jin dadin zamansa a Leeds United kuma ba shi da niyyar barin kungiyar ta Elland Road, in ji wakilinsa. (Jaridar The i )

Chelsea da Arsenal na sa ido a kan dan wasan Bayern Leverkusen, kuma dan tawagar Burkina Faso, Edmond Tapsoba. Sai dai dan wasan bayan mai shekara 22, ya sheda wa 'yan jarida cewa babu wata kwakkwarar magana, ko tattaunawa a hukumance game da hakan, kuma ya ce zai fara kaka mai zuwa a kungiyar ta Jamus. (Jaridar Metro)

Aston Villa ta yi amanna cinikin dan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe zai tabbata, domin za ta yi tayi na uku a kan dan wasan dan Ingila mai shekara 20. (Jaridar Football Insider)

Har yanzu Arsenal ba ta hakura da neman dan bayan Brighton Ben White, mai shekara 23, ba, bayan da ta taya dan wasan na tawagar Ingila fam miliyan 50. Rahotanni sun bayyana maganar cewa cinikin ya fada a haka a matsayin tsabar shirme. (Argus)

Southampton na da kwarin guiwa za ta samu aron dan bayan Manchester United Brandon Williams domin taka mata leda a kaka mai kamawa. Kungiyar ta Saints ta zaku ta samu dan wasan dan Ingila mai shekara 20 a bazarar da ta wuce amma kuma United ta ki bayar da shi saboda kwazonsa a kakar. (Mail)

Burnley ta nuna sha'awar daukar mai tsaron raga Wayne Hennessey. Golan na Wales mai shekara 34, wanda ba shi da wata kungiya, zabi ne ga Chelsea da Aston Villa bayan barinsa Crystal Palace lokacin da kwantiraginsa ya kare a watan da ya wuce. (Mail)

Lionel Messi ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or fiye da kowa ne dan wasa - guda shida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or fiye da kowanne dan wasa a duniya

Barcelona za ta ba wa Chelsea damar sayen dan gabanta Antoine Griezmann. Kungiyar ta Kataloniya da ke fama da karancin kudi na kokarin ganin yadda za ta samu kudin da za ta rika biyan Lionel Messi, na sabon kwantiragi, saboda haka take neman yadda za ta sayar da dan wasan na Faransa mai shekara 30. (Jaridar Star)

Sai dai shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce komai na tafiya dai-dai duk da cewa kwantiragin Messi mai shekara 34 da kungiyar ya kare. (Jaridar Marca)

Antoine Griezmann

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Antoine Griezmann

Manchester United da Arsenal na kokarin dauko dan bayan Barcelona Samuel Umtiti. Dan wasan na Faransa mai shekara 27 ba ya cikin tsarin kociyan kungiyar Ronald Koeman. (Jaridar Star)