Ana aikin gayya a Kano domin kaucewa ambaliyar ruwa

Wasu mazauna jihar Kano da ke arewacin Najeriya, sun fara duƙufa wajen aikin gayya don yashe magudanan ruwa a yankunansu, kafin damunar bana ta kankama.
Kano na cikin jihohin ƙasar da ake samun ambaliyar ruwa a lokutan damuna, kuma ko a bara an samu asarar dukiyoyi da rugujewar gidaje a ƙananan hukumomin jihar.
Yawancin wadanda suka fito aikin gayyar da wakilinmu Khalifa Shehu Dokaji ya ci karo da su, sun ce ambaliyar ruwa ta rushe musu gidaje ko kuma ta haddasa musu asarar dukiya.
Samari da dattawa mazauna unguwar Jakada ke birnin Kano ne su ke aikin gayya, na gyaran magudana ruwan dake unguwar da kasa ta cikesu, gabanin ruwan sama na bana ya fara karfi, dan gudun sake samun ambaliyar ruwan da suka fuskanta a shekara data gabata.
Wasu daga cikin masu aikin gayyar sun shaidawa wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji cewar ganin yadda gidajen su suka rushe yasa suka yanke shawarar fara wannan aikin tun daga yanzu.
''Ganin cewa a duk lokacin da damuna ta zo ana samun matsalar cushewar magudanan ruwa, yadda ruwan ke komawa gidajen mutane da haddasa ambaliyar ruwa, sai muka yanke shawarar yin aikin gayya, kuma muka shiga ciki domin karawa matasa kwarin gwiwar yi,'' inji wani mai suna Ya'u Sa'idu.
Shi ma Abdullahi Ado Dorayi cewa ya ke yi ''wannan aikin ya taimaka, babu batun shekaru an samu ambaliyar ruwa a bara, ruwa ya shigar mana gida shi ya sa muka shiga aikin nan, domin ko ni nan dakuna 2 ne suka zube a gidana.''
Tun dai gabanin saukar damunar wannna shekarar hukumomi a Kano irin su hukuma bayar da agajin gaggawa dake jihar ne ke ta kiraye kiraye ga alummar jihar, da su gyaran magudanan ruwa dake unguwaninsu tare da kauracewa zubar da shara da gini akan magudanan ruwa.
Sannan akwai hasashen cewar za'a sami ambaliyar ruwa a jihar Kano, sakamakon mamakon ruwan sama a jihar a kananan hukumomi 25 daga cikin 44 da ake dasu a jihar ciki kuwa har da karamar hukumar cikin birni.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa dake a Kano, Hon Sale Jili ya ce ''saboda hasashen da aka yi a bana jihar Kano na cikin wadanda za su samu ruwan sama mai karfin gaske da iska , ya kai akalla kananan hukumomi 25 da za a samu rusau saboda haka, sai muka dauki matakin kiran mutane su fito su fara kwashe magudanan ruwansu, za mu kuma shirya taro a kananan hukumomin domnin wayar da kan mutane kan hakan ta yadda za a shawo kan matsalar.''
A bara dai hukumomi a Kano sun bayyana cewar anyi asarar dukiyoyi da kadarori masu dimbin yawa a jihar sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a damunar bara data gabata. Inda kananna hukumomi 20 daga cikin 44 dake Kano su ne wannan matsalar tafi shafa sabida mamakon ruwan saman da aka samu a bara.









