Rikicin Isra'ila da Gaza: Hotunan tashin hankali da fargabar da mutane ke ciki

A man stands near a burning sponge factory after it was hit by Israeli artillery shells in Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A factory burns in Gaza after it was hit by Israeli artillery shells
An wallafa

Rikici tsakanin Isra'ila da mayaƙan Falasdinawa bai nuna alamun tsagaitawa ba, yayin da ake ci gaba da nuna fargaba kan yadda tashin hankalin ke shafar fararen hula.

Wasu hotuna masu jan hankali sun nuna yadda rikicin ya haifar da mummunan tasiri a cikin kwanaki kadan da suka gabata, yayin da hare-hare da sama da hare-haren makaman roka suka mayar da gidaje da gidaje buraguzai, tare da tilasta wa mutane neman matsuguni.

A man stands near a burning sponge factory after it was hit by Israeli artillery shells in Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A factory burns in Gaza after it was hit by Israeli artillery shells

Isra'ila ta ce tana kai hare-haren ta sama kan mayakan Hamas a Gaza ne amma sun kuma lalata hanyoyin wutar lantarki da manyan titina.

A hoton da ke sama, wani Bafalasdine ya dafe kai yana kallon yadda gidansa ke cin wuta sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama a ranar Lahadi.

Buraguzan ginin sun binne wasu daga cikin iyalansa.

A woman mourns for her relatives who were killed during an Israeli raid on Gaza City on May 16

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ita ce rana mafi muni a Gaza tun bayan barkewar rikicin fiye da mako ɗaya.

Hare-haren ta sama da Isra'ila ke kai wa sun faɗa kan titi mai cunkosun jama'a bayan tsakar dare, tare da haddasa rushewar gine-gine da dama da hallaka gwamman mutane.

"Muna buƙatar akalla karin shekaru 10 mu sake gina abubuwan da aka lalata a nan Gaza,'' kamar yadda Mohammad Abu Rayya, wani likitan yara ya shaida wa BBC a ranar Litinin bayan hare-haren.

An gudanar da jana'izar wadanda suka mutu a yankin. Matar da ke sama na jimami da alhinin danginta da suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza.

A child walks on stairs inside a bomb shelter in Ashkelon, southern Israel, on May 16

Asalin hoton, Reuters

A nata ɓangaren, kungiyar Hamas da ke rike da ikon Gaza da sauran kungiyoyin Falasdinawa masu ɗauke da makamai da ke ci gaba da ƙaddamar da hare-haren rokoki zuwa kudancin Isra'ila.

An lalata gidaje da gine-gine, kuma miliyoyin ƴan Isra'ila ne aka tilasta wa tsere wa muhallansu yayin da jiniya ke ci gaba da kaɗawa

Wannan yarinyar a hoton da ke sama, an dauki hotonta ne a wani matsuguni a birnin Ashkelon wanda ya sha fama da hare-haren rokoki.

Victoria Tapalashvili checks the damage after a rocket fired from the Gaza Strip hit near her house on May 17

Asalin hoton, Getty Images

Ana iya ganin Victoria Tapalashvili tana duba yadda aka lalata gidanta a birnin Ashdod na kudancin Isra'ila sakamakon harin.

"Ba abu ne mai sauki ba - kusan ko wane yammaci, ko wane dare, mu kan tashi yara daga barci mu ruga neman mafaka," kamar yadda wani ɗan kasar Isra'ila kuma mai ƴaƴa uku Eitan Singer, ya shaida wa BBC.

"Muna da dakikoki 30 zuwa 60 mu nemi mafaka."

A photo taken on May 17, 2021 shows a damaged apartment in a residential neighbourhood in the southern Israeli city of Ashdod

Asalin hoton, AFP

Wannan hoton ya nuna wani gidan da aka lalata a birnin Ashdod.

An bayyana cewa Isra'ila ta kakkabo kashi 90 bisa dari na makaman rokar da aka harba a yankinta.

An kuma harba rokokin daga kudancin kasar Lebanon zuwa arewacin Isra'ila.

Palestinian relatives watch as mourners carry the body of Yaseen Hamad during his funeral in the West Bank on 16 May

Asalin hoton, EPA

Tashin hankalin ya kuma bazu zuwa yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan inda dakarun Isra'ila suka yi arangama da Falasdinawa a ƙarshen mako.

Waɗannan Falasdinawan na kallo daga taga yayin da masu zaman alhini ke daukar gawar wani dan uwansu lokacin jana'iza a Gabar Yamma da Kogin Jordan ranar Lahadi.

Larabawan Falasdinu na zaune a Gabar Yamma da Kogin Jordan a karkashin takaitaccen mulkin kai da kuma mulkin soji na Isra'ila.

Riyad Eshkuntana kisses his daughter Suzy"s hand as they are treated at a hospital after being pulled from the rubble

Asalin hoton, Reuters

Wannan mutumin, Riyad Eshkuntana an janyo shi ne daga cikin buraguzai tare da ƴar shi Suzy mai shekara shida a Gaza.

Ta makale har na tsawon sa'o'i a ƙarƙashin gidansu, kuma daga bisani suka sake haɗuwa da mahaifinta a asibiti mafi girma a Gaza.

"Ki yi min afuwa ƴa ta. Kin yi ta ihu don na zo gare ki, amma na kasa zuwa," Mr Eshkuntana ta shaida mata a lokacin da suka sake haduwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

A member of the Abu Dayer family, surrounded by relatives, cries at the Al-Shifa hospital after the death of his father and cousin in an Israeli air strike

Asalin hoton, Getty Images

Wannan hoton na nuna iyalan Abu Dayer a asibitin Al-Shifa a Gaza, jim kadan bayan mutuwar wasu iyalai biyu.

An Israeli woman reacts as she checks the damage inside her house hit by Palestinian rocket fire in the southern city of Ashkelon

Asalin hoton, AFP

Wannan matar na duba barnar da aka yi wa gidanta a birnin Ashkelon, yayin da daga bayan ta ake ci gaba da bayar da rahoton fadan da ke faruwa.

Tashin hankalin ya haifar da karin damuwa ga kasashen duniya.

Shugabannin kasashen duniya da kungiyoyin bayar da agaji sun yi kira da a dauki matakan kauce wa mace-macen mazauna yankunan da kuma damuwar da aka shiga sakamakon lalata gine-gine da hanyoyi.

The father of 12-year-old Rahaf al-Dayer holds her covered body at al-Shifa hospital, after she was killed in an Israeli airstrike on 17 May

Asalin hoton, Getty Images

A hoton sama, wani mutum na jimamin mutuwar 'yarsa mai shekara 12 a Gaza.

Kuma a hoton ƙasa, iyalai da abokin wani sojan Isra'ila na kuka a lokacin jana'izarsa.

Yanzu rikicin ya shiga mako na biyu, kuma babu alamun kawo karshe. An ci gaba da kai hare-hare ta sama da hare-haren rokoki.

Amurka da sauran manyan kasashen duniya sun nuna goyon bayan tsagaita wuta - amma da alamu hakan bai yi wani tasiri ba.

Family and friends, including Israeli soldiers, mourn during the funeral of Israeli soldier Omer Tabib, who was killed during cross-border fighting with Gaza

Asalin hoton, Reuters

Dukkanin hotuna na da haƙƙin mallaka