Hotunan Afirka na mako 26 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu 2021: Mai koyon harbi, biri mai dan kunne

An wallafa

Wasu daga cikjin ƙayatattun hotunan sassa daban-daban na Afirka:

Wata mace ta shiga mota a Nairobi, babban birnin Kenya, ranar Asabar - kwana guda bayan hukumomi sun tsaurara dokokin kaucewa kamuwa da korona sakamakon samun karuwar mutane da ke mutuwa sanadin Covid-19...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mace ta shiga mota a Nairobi, babban birnin Kenya, ranar Asabar - kwana guda bayan hukumomi sun tsaurara dokokin kaucewa kamuwa da korona sakamakon samun karuwar mutane da ke mutuwa sanadin Covid-19...
A birnin Mombasa ranar Laraba, mutane sun cika makil a kan wata gada da ke hada babban birnin da kuma yankunan gabar teku a yayin da aka dakatar da shiga kwale-kwale a lokutan da aka fi samun cikowar jama'a a yunkurin dakile yaduwar Covid.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A birnin Mombasa ranar Laraba, mutane sun cika makil a kan wata gada da ke hada babban birnin da kuma yankunan gabar teku a yayin da aka dakatar da shiga kwale-kwale a lokutan da aka fi samun cikowar jama'a a yunkurin dakile yaduwar Covid.
Wani mutum da ke sayar da sarewa a wajen filin wasa da ke birnin Lagos na Najeriya ranar Asabar a yayin wasan neman gurbin shiga Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da Najeriya ta fafata da Lesotho...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum da ke sayar da sarewa a wajen filin wasa da ke birnin Lagos na Najeriya ranar Asabar a yayin wasan neman gurbin shiga Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da Najeriya ta fafata da Lesotho...
An rika bayar da tazara tsakanin masu kallo a cikin filin wasan wanda Super Eagles ta yi nasara da ci 3-0.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An rika bayar da tazara tsakanin masu kallo a cikin filin wasan wanda Super Eagles ta yi nasara da ci 3-0.
A ranar ce kuma a Addis Ababa, magoya baya suka fantsama kan tituna domin yin murna saboda gurbin da Ethiopia ta samu na zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a shekara mai zuwa, karon farkon tun 2013...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar ce kuma a Addis Ababa, magoya baya suka fantsama kan tituna domin yin murna saboda gurbin da Ethiopia ta samu na zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a shekara mai zuwa, karon farkon tun 2013...
Ethiopia ta sha kasi a hannun Ivory Coast kafin a dakatar da wasan bayan lafari ya fadi. Tashin da aka yi babu ci tsaanin Madagascar da Jamhuriyar Nijar ya sa Ethiopia ta sama gurbin zuwa gasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ethiopia ta sha kashi a hannun Ivory Coast kafin a dakatar da wasan bayan lafari ya fadi. Tashin da aka yi babu ci tsakanin Madagascar da Jamhuriyar Nijar ya sa Ethiopia ta sama gurbin zuwa gasar
A Abidjan, babban birnin Ivory Coast washegari wani mai goyon bayan Laurent Gbagbo - wanda ya nuna hakan ta hanyar takalminsa - ya yi ta murna bayan kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ta wanke tsohon shugaban kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Abidjan, babban birnin Ivory Coast washegari wani mai goyon bayan Laurent Gbagbo - wanda ya nuna hakan ta hanyar takalminsa - ya yi ta murna bayan kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ta wanke tsohon shugaban kasar.
Ranar Laraba, an hango wadannan mutanen biyu a wajen wani masallaci a Timbuktu kwana guda bayan an bai wa gwamnatin Mali da Unesco euro a matsayin alamar karramawa. Hakan ya faru ne bayan shari'ar kotun ICC wadda ta samu wani mai ikirarin jihadi da laifin rusa wuraren tarihi a birnin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba, an hango wadannan mutanen biyu a wajen wani masallaci a Timbuktu kwana guda bayan an bai wa gwamnatin Mali da Unesco euro a matsayin alamar karramawa. Hakan ya faru ne bayan shari'ar kotun ICC wadda ta samu wani mai ikirarin jihadi da laifin rusa wuraren tarihi a birnin.
Mai zane Yassine Balbzioui yana tsaye kusa da abin da ya zana ranar Talata a wani bangare na bikin nunin zane-zane da aka yi a Madrid, babban birnin Sifaniya, abin da ke fito da muhimancin zane-zanen kasar Morocco tun shekarar 1950.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mai zane Yassine Balbzioui yana tsaye kusa da abin da ya zana ranar Talata a wani bangare na bikin nunin zane-zane da aka yi a Madrid, babban birnin Sifaniya, abin da ke fito da muhimancin zane-zanen kasar Morocco tun shekarar 1950.
Dan kasar Kamaru Francis Ngannou ya doke Stipe Miocic dan kasar Amurka ranar Asabar inda ya zama sabon zakaran dambe ajin masu naiyu lokacin gasar damben UFC 260 a Las Vegas.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan kasar Kamaru Francis Ngannou ya doke Stipe Miocic dan kasar Amurka ranar Asabar inda ya zama sabon zakaran dambe ajin masu naiyu lokacin gasar damben UFC 260 a Las Vegas.
Kwana biyu bayan haka, 'yan dambe a Senegal sun yi wanka da kasa gabanin atisaye…

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana biyu bayan haka, 'yan kokuwa a Senegal sun yi wanka da kasa gabanin atisaye…
Yanzu 'yan dambe za su iya ci gaba da shirin shiga gasa sakamakon janye dokar korona.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yanzu 'yan kokuwa za su iya ci gaba da shirin shiga gasa sakamakon janye dokar korona.
Masu aikin sa kai suna debe datti daga gabar teku a Lagos ranar Asabar..

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu aikin sa kai suna debe datti daga gabar teku a Lagos ranar Asabar..
A washegari ne a birnin na Lagos, wannan mutumin da 'yarsa suka halarci biki Kiristoci mabiya darikar Katolika suka yi na Palm Sunday inda aka ba su ganyen kwakwa domin tuna musu ranar da Yesu ya isa birnin Qudus kwanaki kafin mutuwarsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A washegari ne a birnin na Lagos, wannan mutumin da 'yarsa suka halarci biki Kiristoci mabiya darikar Katolika suka yi na Palm Sunday inda aka ba su ganyen kwakwa domin tuna musu ranar da Yesu ya isa birnin Qudus kwanaki kafin mutuwarsa.
Ranar Talata aka fitar da hoton wannan matar 'yar kasuwa mai shekara 50 a Ilorin. Yana cikin hotunan da Reuters ta dauka a makon jiya a kan Shade Ajayi wadda ba ta je makaranta ba lokacin tana karama - kuma ta yi amannar cewa rashin karatu da rubutu yana yin tasiri a rayuwarta.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Talata aka fitar da hoton wannan matar 'yar kasuwa mai shekara 50 a Ilorin. Yana cikin hotunan da Reuters ta dauka a makon jiya a kan Shade Ajayi wadda ba ta je makaranta ba lokacin tana karama - kuma ta yi amannar cewa rashin karatu da rubutu yana yin tasiri a rayuwarta.
Ranar Litinin, taron masu jaje a Antananarivo, babban birnin Madagasca, sun rika daga hannayensu ga tawagar jana'izar tsohon shugaban kasa Didier Ratsiraka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin, taron masu jaje a Antananarivo, babban birnin Madagasca, sun rika daga hannayensu ga tawagar jana'izar tsohon shugaban kasa Didier Ratsiraka
A ranar ce kuma a arewacin Mozambique, an hango wadannan kwale-kwalen a Paquitequete, tashar jiragen ruwa da ke kudancin Palma - garin da masu ikirarin jihadi suka kai wa hari a makon jiya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ce kuma a arewacin Mozambique, an hango wadannan kwale-kwalen a Paquitequete, tashar jiragen ruwa da ke kudancin Palma - garin da masu ikirarin jihadi suka kai wa hari a makon jiya.
Har yanzu mutane suna yunkurin tserewa daga yankin, inda cibiya ce ta aikin iskar gas. A wannan hoton, mata ne a Pemba suke rarrashin suna ranar Alhamis a yayin da suke jiran wadanda aka ceto

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Har yanzu mutane suna yunkurin tserewa daga yankin, inda cibiya ce ta aikin iskar gas. A wannan hoton, mata ne a Pemba suke rarrashin suna ranar Alhamis a yayin da suke jiran wadanda aka ceto
Wadannan mutane sanye da tufafin gargajiya sun taru a wajen babban shagon sayar da kaya a Afirka ta Kudu ranar Talata domin yin zanga-zanga bayan an umarci wani mutum sanye da tufafin Ndebele ya bar shagon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wadannan mutane sanye da tufafin gargajiya sun taru a wajen babban shagon sayar da kaya a Afirka ta Kudu ranar Talata domin yin zanga-zanga bayan an umarci wani mutum sanye da tufafin Ndebele ya bar shagon
Ranar Asabar, wadannan matan sun rika koyon harbin bindga a Ekurhuleni da ke Afirka ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Asabar, wadannan matan sun rika koyon harbin bindga a Ekurhuleni da ke Afirka ta Kudu
Su ma gwanayen rawa a Afirka ta Kudu, sun koma atisaye ranar Alhamis a yayin da kamfanin Joburg Ballet ke shirin komawa bakin aiki a makon gobe bayan dogon hutun da ya dauka sakamakon annobar Covid-19.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Su ma gwanayen rawa a Afirka ta Kudu, sun koma atisaye ranar Alhamis a yayin da kamfanin Joburg Ballet ke shirin komawa bakin aiki a makon gobe bayan dogon hutun da ya dauka sakamakon annobar Covid-19.
Ranar Alhamis masu bincike a Jami'ar St Andrews da ke Birtaniya sun fitar da hoton wannan birnin sanye da "dan kunne" ciyawa a Zambia - abin da suka ce wata hanya ce da dabbobi suke nuna dabi'arsu da kuma kwalliya.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Ranar Alhamis masu bincike a Jami'ar St Andrews da ke Birtaniya sun fitar da hoton wannan birnin sanye da "dan kunne" ciyawa a Zambia - abin da suka ce wata hanya ce da dabbobi suke nuna dabi'arsu da kuma kwalliya.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka