An gargaɗi Iran kan ƙera ƙarfen uranium domin samar da makaman nukiliya

A handout photo made available by the Atomic Energy Organisation of Iran shows Iranian Parliamentary speaker Mohammad Baqer Qalibaf (L) and head of Atomic Energy Organisation of Iran Ali Akbar Salehi (2nd L) visiting the Fordo enrichment facility in Iran (28 January 2021)

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Iran ta soma samar da karfen uranium, duk da gargadin da kasashen Yammacin duniya suka yi mata cewa yin hakan tamkar keta yarjejeniyar makamin nukiliya ce da aka rattabawa hannu a 2015.

Masu bincike na hukumar da ke sanya ido kan makamashi ta duniya sun tabbatar cewa kasar tana da 3.6g (0.1oz) na sinadarin a tasharta da ke Isfahan a makon jiya.

Iran ta ce tana gudanar da bincike kuma tana samar da karfen ne da zummar samar da fetur da masu bincike suke amfani da shi.

Sai dai ana iya amfani da karfen uranium wajen hada bom na nukiliya.

Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma ta yi watsi da yarjeniyoyi da dama game da kera makaman nukiliya a shekaru biyu da suka wuce.

Ta ce tana yin hakan ne domin martani ga jerin takunkuman karya tattalin arzikin da gwamnatin Amurka karkashin jagoranci Donald Trump ta sanya mata a 2018 lokacin da ya yi watsi da jarjejeniyar da aka kulla.

Mutumin da ya gaje shi, Joe Biden, ya ce dole ne Iran ta yi biyayya ga dukkan yarjejeniyar da aka kulla idan tana so ya janye mata takunkuman. Sai dai shugaban Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce dole Amurka ta soma janye takunkuman da ta sanya mata kafin ita ma ta dakatar da abin da take yi.

A yarjejeniyar da aka kulla, Iran ta amince ba za ta samar da karfen uranium ko kuma ta gudanar da bincike don bunkasa uranium ba nan da shekara 15.

Ranar Laraba da yamma, hukumar da ke sanya ido kan makamashi ta duniya (IAEA) ta ce darakta janar dinta ya sanar da kasahen da ke cikinta "game da abubuwan da suka faru a baya bayan nan a kan shirin Iran na samar da karfen uranium a wani bangaren shirinta na samar da fetur da zai yi aiki a Cibiyar Bincike kan Madaukin Makaman Nukiliya da ke Tehran".

A handout photo made available by the Atomic Energy Organisation of Iran shows Iranian Parliamentary speaker Mohammad Baqer Qalibaf (L) and head of Atomic Energy Organisation of Iran Ali Akbar Salehi (2nd L) visiting the Fordo enrichment facility in Iran (28 January 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A watan Disamba majalisar dokokin Iran ta amince gwamnati ta hanzarta kamala shirinta na kera makamashin uranium

"Ranar 8 ga watan Fabrairu hukumar ta gano 3.6g na karfen uranium a Cibiyar Samar da Fetur da ke Sarrafa Makamin Nukiliya da ke Isfahan," in ji shi.

A watan jiya, Hukumar Samar da Makamashi ta Iran (AEOI) ta ce ta soma gudanar da aiki na samar da fetur da ake kira silicide Cibiyar lura da Madaukin makamin nukiliya ta Tehran, wanda aka dora wa alhakin samar da hotunan da suka jibanci harkokin lafiya.

Hukumar ta AEOI ta dage cewa ana samar da karfen uranium kacokan domin ayyukan zaman lafiya, tana mai cewa ba ta keta wata yarjejeniyar kasashen duniya kan kera makaman nukiliya ba.

Birtaniya, Faransa da Jamus - manyan kasashen duniya uku cikin biyar da har yanzu ke cikin yarjejeniyar nukiliya - sun ce sun yi "matukar damuwa" da jin sanarwar da Iran ta fitar kan batun.

Sun yi gargadin cewa: "Iran ba ta da wata hujja ta samar da karfen uranium. Samar da karfen uranium zai iya jawo da martani na soji."

A watan Disamba, majalisar dokokin Iran ta amince da wani kudurin doka da ya bukaci gwamnati kammala tashar kera makamin uranium da ke Isfahancikin watanni biyar.

'Yan majalisa masu tsattsauran ra'ayi sun gabatar da kudurin ne bayan kisan da Isra'ila ta yi wa wani masanin nukiliya Mohsen Fakhrizadeh a watan Nuwamba.

Iranian troops carry the coffin of assassinated nuclear scientist Mohsen Fakhrizadeh in Tehran, Iran (30 November 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Iranta dora alhakin kisan Mohsen Fakhrizadeh kan Isra'ila