Kasar Iran ta sanar da komawa shirinta na samar da makamashin nukiliya

Kasar Iran ta shaida wa hukuma mai sanya ido kan makaman nukiliya ta duniya, IAEA cewa tana shirin fara sarrafa sinadarin Uranium fiye da yadda hukumar ta lamunce da a yi.
Iran dai ta dade tana karya wani bangare na dokar makaman na nukiliya, to sai dai ana yi wa barazanar ta yanzu kallon wuce-gona da iri.
Hukumar ta IAEA ta ce Iraniyawa sun sanar da ita cewa sun kudiri niyyar fara sarrafa sinadarin na Uranium zuwa kaso 20 na ma'aunin inganci.
Hakan kuwa ya gaza kaso 90 da ake bukata domin samar da makaman nukiliya kwarai da aniya.
To sai dai bisa yarjejeniyar nukiliya ta duniya, bai kamata Iran ta gota kaso hudu ba na sarrafa sinadarin.
Babu tantama cewa shirin Iran din na kokarin inganta Uranium zai tunzira kasashen da ke son taka wa shirinta na samar makamin nukiliya burki.
A 2018 ne dai shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump ya kekketa takardar yarjejeniyar ya kuma sanar da ficewa.
Mista Trump ya kuma sake kakaba wa Iran din jerin takunkumin karya tattalin arziki masu zafin gaske.
To sai dai maimakon Iran din ta saduda sai ta kara kaimi wajen saba iyakokin da aka gindaya mata a cikin yarjejeniyar.
A watan jiya ne hankalin Iraniyawa ya tashi sakamakon kisan fitaccen masanin kimiyyar makamin nukiliyar kasar da ta zargi kasar Isra'ila da yi.
Kuma hakan ne ya sa majalisar dokokin Iran din ta nemi da aka matsa gaba wajen sarrafa Uranium din zuwa kaso 20 ma'aunin inganci.











