Fafaroma Francis ya naɗa mace ta farko cikin majalisar bishop-bishop

Asalin hoton, EPA
A karon farko Fafaroma Francis ya naɗa wata mata a matsayin babbar jami'a a majalisar bishop-bishop ɗin majalisar ƙoli ta cocin Katolika.
Sister Nathalie Becquart, wadda ƴar ƙasar Faransa ce, za ta sami dukkan ikon da sauran ƴan kwamitin maza ke da shi.
Kwamitin ne ke da alhakin ba Fafaroma shawara kan batutuwa masu sarkakiya da ke fuskantar cocin Roman Katolika.
Tun 2019 Ms Becquart ke aiki da kwamitin a matsayin kwararriya kan batutuwan siyasar duniya da yadda yake shafar cocon na Katolika.
Babban sakataren majalisar Cardinal Mario Grech ya ce naɗin da a ka yi wa wannan matar na nufin an "buɗe wata kofa ke nan."
Ya kuma lura cewa Fafaroman na da sha'awar ganin "mata na taka rawar gani kan yadda ake nazari da yanke hukunci a cocin".
Wakilin BBC John McManus ya ce wannan matakin ba yana nufin cocin zai fara naɗa mata ga mukamin fada-fada ba ne, amma wasu mabiya na iya kallon matakin da wannan fahimtar.
Fafaroman ya kuma naɗa Luis Marín de San Martín, wanda fada ne daga ƙasar Spaniya, a matsayin sabon ƙaramin sakataren majalisar ta bishop-bishop.
A 'yan shekarun nan, majalisar ta bishop-bishop, ko Synod of Bishops da turancin Ingilishi ya yi nazari kan batutuwan da suka haɗa da yadda ake mu'amala da mabiya ɗarikar ta Katolika da suka kashe aurensu da waɗanda ke da aure.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Wannan naɗin na zuwa ne ƙasa da wata guda da Fafroma Francis ya sanar da cewa ya sauya dokokin cocin, musamman wadda ta shafi ba mata damar yin wasu muhimman ayyukan ibada da zama a mumbarin coci, amma sabuwar dokar ba ta ba mata damar zama fada-fada ba.
Har yanzu maza ne ke da wannan damar ke nan.










