Coronavirus: Kada ku ba da kai ga tsoro - Fafaroma Francis

Pope Francis leads the Easter Vigil in the Holy Night of Easter in St. Peter's Basilica

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis ya yi kira ga mutane su kasance "manzannin rayuwa a lokacin mutuwa"
An wallafa

Fafaroma Francis ya bukaci jama'a kada su "muka kai ga tsoro" kan cutar coronavirus, inda ya bukaci su kasance "mazannin rayuwa a lokacin mutuwa".

Jagoran na Cocin Roman Katolika na jawabi ne yayin gudanar da addu'o'in kwanan zaune na daren Ista a zauren Cocin St Peter da kusan yake wayam.

Mabiya darikar katolika a fadin duniya kimanin biliyan 1 da miliyan 300 na iya kallon jawabinsa na ranar Ista da za a nuna kai tsaye ta intanet.

Ista dai, biki ne mafi muhimmanci a kalandar mabiya addinin kirista - kuma suna bikin ne don murnar sake tashin Yesu Almasihu kwana uku bayan gicciye shi.

Bisa al'ada dumbin masu bi kan cika zaurukan coci-coci da mujami'u, yayin da dubun dubatar wasu kan makare Dandalin St Peter a fadar Vatican.

Sai dai a bana duk wannan ta sauya saboda annobar koronabairas.

An tsara nuna jawabin da Fafaroma ya saba gabatarwa duk shekara a ranar Ista kai tsaye ta intanet daga wani dakin karatunsa - yayin da Italiyawa ke ci gaba da zaman kulle a gidajensu.

Pope Francis attends the Easter vigil Mass

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan gomman mutane ne suka halarci addu'o'in kwanan zaune na daren Ista da Fafaroma ya gudanar

Da yake gudanar da addu'o'in kwanan zaune na daren Ista a mujami'ar St Peter wadda kusan take wayam, Fafaroma Francis dai ya nanata sakon kyautata fata.

"Kada ku yi fargaba, kada ku ba da kai ga tsoro. Wannan sakon fatan alheri ne, in ji shi.

Ya ce "Wannan ranar, tamu ce. Wadannan ne kalaman da Ubangiji ya jadadda mana cikin daren nan.

A wannan dare mun yi nasarar samun 'yancin da ba wanda zai iya karbe mana. wato 'Yancin kyakkyawan fata!

Nan gaba a yau ne kuma Fafaroma Francis zai gabatar da jawabin Ista da kuma addu'o'in sanya albarka a gaban wani dan kankanin taro -- maimakon makeken cincirindon jama'a da galibi kan cika makil a dandalin St Peter.

A Amurka, masu ibada na gudanar da addu'o'in ranar Ista ne daga cikin motocinsu bayan sun taru a filayen ajiye motoci da kuma silimun da ake kallo daga cikin mota.