Lafiya Zinariya: Rawar da kungiyoyi ke takawa wajen taimaka wa masu larurar amosanin jini
Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren shirin na Lafiya Zinariya:
Likitoci sun bayyana cutar amosanin jini da cewa cuta ce da ke tagayyara masu fama da ita.
Dr. Maryam Mahdi, wata likita da ke aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Tabawa Balewa da ke jihar Bauchi, a arewa-maso-gabashin Najeriya.
Ta shaida wa BBC cewa ko da yake mafiya yawan masu cutar sikila kan rungumi kaddara, amma wasu su kan fada cikin matsananciyar damuwa, lamarin da kan sa su yi yunkurin kashe kansu.
Likitar ta kara da cewa idan uwa da uba sun kasance AS wato suna dauke da wani bangare na cutar amosanin jini to akwai yiwuwar su haifi 'ya'ya SS wato masu sikila.
A duk shekara ana haihuwar masu wannan cuta kimanin dubu dari uku a fadin duniya.
Yayin da kashi biyu bisa uku na wadannan yara suna nahiyar Afrika.
Najeriya dai ita ce kasar da ta fi kowacce yawan masu cutar amosanin jini a duniya.
Sai dai a cewarta har yanzu mutane ba sa yin gwajin jini kafin aure, wanda hakan ita ce hanya daya ta kaucewa haihuwar 'ya'ya masu cutar.
Daga cikin alamomin cutar a cewar likitar sun hada da ciwon kashi da gabobi da ciwon huhu da kuma a wasu lokutan jininsu na karewa har sai an kara musu jini.
Masu wannan cuta dai na kwashe tsawon rayuwarsu suna shan magunguna domin saukaka matsalolin kiwon lafiyar da suke fuskanta.
Hanya daya ta warkewa daga wannan cuta ita ce ta yin dashen bargo, sai dai kuma tana tattare da hadari, abin da yasa ba kasafai ake yinsa ba.
Ko da yake an samu wasu 'yan mata 'yan Najeriya da aka yi wa wannan dashen a shekarun baya, kuma an samu nasara.














