Lafiya Zinariya: Kalubalen rayuwa da mace mai cutar sikila kan shiga
An wallafa
Larura ta rashin lafiya abu ne da kan sami ko wane dan adam daga lokaci zuwa wani lokaci a cikin rayuwarsa.
Sai dai ko ya za ka ji idan a karon farko ka san cewa kana dauke da cutar da ba za ka warke ba a tsawon rayuwarka?
Cutar amosanin jini ko sikila cuta ce wadda likitoci suka ce za a iya kauce masa ta hanyar yin gwaji kafin a yi aure.
Amma nan gizo ke sakar domin har yanzu a wasu kasashen Afrika ciki har da Najeriya ba kasafai mutane ke amfani da wannan shawara ba.
A wannan makon Habiba Adamu ta yi mana nazari kan wannan cutar, ga kuma rahoton da ta hada mana: