FBI ga Amurkawa: Magoya bayan Trump na shirin kai hare-hare

Members of the National Guard stand next to a fence and barricades set up around the U.S. Capitol building in Washingto

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An tsaurara matakan tsaro a majalisar Amurka bayan kutsen da magoya bayan Mista Trump suka yi a makon jiya
An wallafa

Hukumar tsaro ta FBI ta gargadin Amurkawa da su zama cikin shiri domin sun gano magoya bayan shugaba Trump na shirin fara wasu jerin zanga-zanga a fadin kasar gabanin rantsar da Joe Biden.

Hakan ne ya sa aka dauki karin matakan tsaro a birnin Washington DC. An jibge jami'an 'yan sanda da na soji a sassa daban-daban na birnin.

FBI ta ce ta samu bayanan da ke nuna cewa magoya bayan Shugaban Amurka Donald Trump ba su saduda ba - domin a halin da ake ciki, suna kitsa wani gagarumin shiri na yunkurin hana a rantsar da zababben shugaba Joe Biden a gaban majalisar kasar.

Majalisar da a makon jiya su ka kai wani mummunan samame har ta kai ga mutum shida sun rasa rayukansu.

Jami'an tsaro na cikin gida kan kulle wani bangare na birnin Washington ana kwana guda gabanin a gudanar da bikin. Amma saboda barazanar da ake fuskanta, za su kulle yawancin birnin ne tun ranar Laraba, kwana shida kafin ranar bikin.

Za a baza jami'an soji 10,000 na ko-ta-kwana wato National Guard a birnin, inda za su yi aiki kafada da kafada da sauran jami'an tsaro na gwamnatin tarayya da na jihohi karkashin wata cibiya ta hadin gwuiwa.

A wani bangaren kuma, Magajin Garin Washington Muriel Bowser ta dakatar da ba mutane izinin shiga dukkan wuraren shakatawa na cikin birnin domin rage yawan mutanen da za su iya kwarara zuwa wajen bikin.

Gwamnonin jihohi biyu da ke makwabtaka da babban birnin na Washington DC suna ta yin kira ga al'umominsu da su yi zamansu a gida.

Ama duk da wannan barazanarr ta tsaro, jami'an 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kuma suna ta ganowa ada damke wasu daga cikin magoya bayan shugaba Trump da suka afka wa ginin majalisar kasar wanda aka fi sani da Capitol.

'Yan majalisar kasar kuma karkashin jagorancin Nancy Pelosi, kakakin majalisar wakilan kasar da jam'iyyar Democrat an ci gaba da shirinsu na tsige shugaba Trump duk da kwanaki kalilan ne su ka rage ya sauka daga mukamin nasa.